Tattaunawar kafa gwamnatin hadin kai Falasdinawa ta kafe | Labarai | DW | 30.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawar kafa gwamnatin hadin kai Falasdinawa ta kafe

Tattaunawar da ake yi tsakanin kungiyoyin Fatah da Hamas da nufin kafa wata gwamnatin hadin kan kasa ta cije. An jiyo haka ne daga bakin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a ganawar da yayi da sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice a birnin Jericho na Gabar Yamma da Kogin Jordan. Rice ta godewa Abbas game da rawar da ya taka wajen kulla shirin tsagaita wuta na baya bayan a Zirin Gaza. Yanzu haka dai Amirka na fatan ganin an fadada shirin tsagaita wutar a dukkan yankunan Falasdinawa. Dr. Rice ta kuma tabo batun kafa wata kasar Falasdinawa mai ´yancinta.