1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar farko tsakanin Kiir da Machar

May 8, 2014

Jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar ya isa kasar Habasha don yin tattaunawar farko da shugaba Salva Kiir tun bayan barkewar rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/1Bwed
Südsudan Juba Riek Machar Salva Kiir 09.07.2013
Hoto: Reuters

Wani babban jami'i na kungiyar kasashen gabacin Afirka, Tewolde Gebremeskel ya ce jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar ya sauka kasar Habasha wato Ethiopia inda zai tattauna da shugaban Suda ta Kudu Salva Kiir. Gebremeskel ya ce Machal ya isa a birnin Gambella na kasar Habasha inda a wannan Jumma'a za a gudanar da tattaunawar farko tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu tun bayan barkewar rikicin kasar a cikin watan Disamban bara. Rikicin dai da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, sannan wasu kimanin miliyan 1.3 sun tsere daga gidajensu. Ma'aikatan agaji sun nuna fargabar barkewar annobar matsananciyar yunwa idan ba a kawo karshen rikicin kuma mutane suka yi shuka ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman