Tattaunawa ta ci tura tsakanin shugabanin Israila dana Palasdinawa | Labarai | DW | 15.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa ta ci tura tsakanin shugabanin Israila dana Palasdinawa

P/M Israila Ehud Olmert ya sanar da cewa yunƙurin ganawa tsakanin sa da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ta ci tura. Wani jamií a Ofishin P/M na Israila ya ruwaito cewa Mahmoud Abbas na buƙatar a sako fursunonin Palasdinu a matsayin sharaɗi kafin ganawar. Olmert yace babu wani fursuna da Israilan zata sako har sai yan takifen Hamas sun sako sojin Israila Kopur Gilad Shalit da suka yi garkuwa da shi a watan yunin da ya gabata. Ya ƙara da cewa a shirye suke su gana da Abu Mazen to amma ga alama bashi da shaawar hakan.