Tattaunawa kan rikicin Bangui ya cije | Labarai | DW | 10.01.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa kan rikicin Bangui ya cije

Bisa ga dukkan alamu da saura wajen shawo kan faɗa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda yan tawaye da gwamnati ko yaƙi yin sassuci

Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service Soldiers from the Chadian contingent of the Central African Multinational Force (FOMAC) hold their weapons as they patrol in Damara, about 75 km (46 miles) north of Bangui January 2, 2013. Rebels in Central African Republic said they had halted their advance on the capital on Wednesday and agreed to start peace talks, averting a clash with regionally backed troops in the mineral-rich nation. REUTERS/Luc Gnago (CENTRAL AFRICAN REPUBLIC - Tags: MILITARY CIVIL UNREST POLITICS)

Sojan kasar Cadi da suka kai ɗauki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Tattaunawa kan rikicin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya tashi ba tareda tsinan komai ba, inda aka tashi ba tare da yan tawaye da gwamnati sun amince da tsagaita wuta ba. Tattaunawar farko ta ƙare a jiya Laraba, ba tare da ko wane bangare ya nuna alamar ajeyi makami ba, a fadan da aka yi wata guda ana yi. Su dai yan tawayen ƙungiyar Seleka sun buƙaci shugaba Francois Bozize da ya yi murabus. Dama dai ƙungiyar ƙasashen yakin tsakiyar Afirka tare tallafin MDD da ƙasar Amirka suka shirya tattaunawar. Da farko dai an yi zaton farfado da yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta 2007, amma yan tawaye suka ce wacan tattaunawa shugaba Bozize ya saɓa mata. Za dai aci gaba da ƙoƙarin shawo kan ɓangororin biyu a wata sabuwar tattauanwar a yau Alhamis.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu

 • Kwanan wata 10.01.2013
 • Mawallafi Usman Shehu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17Gw5
 • Kwanan wata 10.01.2013
 • Mawallafi Usman Shehu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17Gw5