Tattaunawa da tsagerun Niger Delta don shawo kan matsalar hare-hare | Siyasa | DW | 07.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tattaunawa da tsagerun Niger Delta don shawo kan matsalar hare-hare

Matakin gwamnatin Najeriya na tattaunawa da Niger Delta Avengers na cin karo da martanin kwarraru a fannin tsaro.

Wannan shawara da gwamnatin Najeriyar ta yanke don tattaunawa da tsagerun na Niger Delta Avengers ya sa tuni har gwamnati ta kafa kwamiti na musamman da zai tabbatar da batun bin hanya ta lalama bayan cigaba da amfani da karfi irin na soja a kan wannan sabuwar kungiya. Ta dai kara kaimin kai hare-hare tare ma da fitar da barazana ta kai hari da makami mai linzami har zuwa Abuja da ake wa kalon tudun na tsira daga irin wadannan matsaloli.

Ministan kasa a ma'aikatar kula da harkokin mai Ibeh Kachikwu da ya sanar da hakan ya ce tuni har an kafa kwamiti da zai bi hanyar tattaunawa a daidai lokacin da suke amfani da karfin soja, da bayanai ke nuna gwamnati na son rage shi sannnu a hankali. To ko me wannan ke nunawa? Air Commodore Yusuf Anas mai ritaya kwararre ne a kan wannan harka kuma ma shi ne shugaban cibiyar sadarwa a kan rigingimu irin na yankin ya bayyana cewa.

"Wannan mataki da gwamnati ta dauka ya yi daidai, domin idan aka samu matsala irin wannan a kasa, ko da an yi amfani da karfi soja, daga baya za a koma kan teburin sulhu ne."

Koma a kan bin hanyar sulhu ga 'ya'yan kungiyar ta yankin Niger Delta ai ya biyo bayan sake maido da su don su cigaba da samar da tsaro ga bututun mai bayan da gwamnati ta karbe aikin daga hannunsu abinda suka yi watsi da shi.

Shawo kan musabbabin matsalolin Niger Delta

Ga 'yan asalin yankin da suka dade suna fafutuka da gwagwarmaya irin su Nnimo Bassey na kungiyar alkinta muhalli na mai bayyana cewa.

"Dole ne a fara shawo kan zahirin matsalolin da suka haifar da rigingimu na tsageranci a yankin Niger Delta kafin a yi komai ba wai maganar cusa siyasa a al'amarin ba. Ba wai bama son kayan more rayuwa ba ne, amma in ka gina kuma muhallin babu wani ci gaba fa? A bai wa mutane damar su koma aikin da suka fi sani na kamun kifi, noma da sauransu. Duk lokacin da mutane suka duba yanayin rasuyarsu sai su harzuka."

Nigeria Militär-Patrouillen im Niger-Delta

Sojojin Najeriya na cigaba da sintiri a yankin na Niger Delta

A lokutan baya dai kokarin gwama amfani da karfi irin na soja da kuma hanyar lalama ya kasance wanda ake wa kalon mai kamar wuya ga yanayi irin Najeriya. Ko wane tasiri wannan zai yi wajen shawo kan kungiyar da ke fitar da sabbin barazana har da na kai hari da makami mai linzami? Har ila yau ga Air Commodore Yusuf Anas mai ritaya.

"Kasancewa wasu daga cikinsu duk da kiraye-kirayen da aka yi da su daina, har yanzu suna cigaba da aikace-aikacen da zan kira ta'addanci. To ka ga ke nan ya zama dole a yi amfani da karfi a wani lokacin kafin a samu biyan bukata."

Öl Industrie in Nigeria

Hare-hare kan bututan mai ya janyo wa kasar asarar babba

Sannu a hankali dai hare-haren da sabuwar kungiyar ta Niger Delta Avengers da ke hai hare-hare irin na ta'addanci ga tattalin arzikin Najeriya sun haddasa illar da ta sanya fuskantar raguwar man da Najeriya ke fitarwa daga sama da ganga miliyan biyu zuwa ganga miliyan 1.6. Yanzu dai abin jira a gani shi ne tasirin da wannan matakin zai yi ga kokarin shawo kan matsalar.

Sauti da bidiyo akan labarin