1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin Najeriya na tangal-tangal

Ubale Musa/GATDecember 17, 2015

Kasa da mako guda da gabatar da sabon kasafin kudin tarayyar Najeriya na badi da ya kai triliyan shida, daga dukkan alamu har yanzu kasar fiskantar kalubale na neman hanyoyin tara kudin.

https://p.dw.com/p/1HPPO
Nigeria Muhammadu Buhari Präsident Rede vor der UN Vollversammlung
Hoto: Getty Images/AFP/M. Ngan

Kasa da mako guda da gabatar da sabon kasafin kudin tarayyar Najeriya na badi, daga dukkan alamu har yanzu tana kasa tana dabo ga kasar da ta yi kasafin triliyan shida amma kuma ke fuskantar kalubale na neman hanyoyin tara kudin.Alaman tana shirin yin tsauri ga kasar da ke dogaro da man fetur domin hali na rayuwa na dada bayyana a halin yanzu, sakamakon ta ci ba ta cin dake neman mamaye harkokin kudin kasar a halin yanzu.

A talatar makon gobe ne dai shugaban kasar yake shirin kai kasafin mafi girma a cikin tarihi na kasar a gaban majalisun tarrayar da nufin nazari dama amincewa kanta.To sai dai kuma tuni alamun karyewar kasafin ta fara bayyana sakamakon karin rushewa ta tattalin arzikin kasar a halin yanzu.

Duk da cewar dai an dora kasafin a bisa dalar Amirka 38 kan kowace ganga tuni man ya fara nuna alamar rushewa tare da makomawar farashin ya zuwa dala 37 ya zuwa yammacin wannan Alhamis. Ko bayan nan dai ita kanta gangar man miliyan biyu za ta kai ga samar da triliyan hudu a cikin shidan da kasar ke fata na kashewa da nufin nuna alamun sauyi na rayuwar al'umma.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Hoto: Getty Images

Tuni dai wani taron majalisar tattalin arziki ta kasar da yammacin wannan Alhamis a Abuja ya fara duban mafita da nufin iya cika alkawarin da 'yan kasar ke zaman jiran gani cikin kasa a halin yanzu, kuma a fadar Atiku Bagudu da ke zaman gwamnan jihar Kebi ya sanya neman mafita a tsakanin matakai daban-daban na kasar da nufin fitar da A´i cikin ramar dake neman sarke ta a yanzu.

"Tun watanni hudu da suka gabata aka faradaukar matakai saboda Shugaba Buhari da babban bankin Najeriya sun ba da gudummawa ga jihohi da kamfanoni masu neman su yi aikin noma musamman na shikafa da alkama.Wannan hange ne da aka yi cewa kasuwar mai da ake dogara da ita ba za ta dauwama ba. Dan haka aka dauki mataki na samar wa da mutane hanyar samun kudin shiga dama canza tunani na dogara da harakar mai. Dan haka abin da muka gani yau shi ne kasuwar tana yin sama da kasa, amma wannan tsarin da aka dauko tafiya ta hau hanya"

Ko ya zuwa ina kasar take shirin cika gibin da ya kai kusan kaso 30 cikin dari na sabon kasafin dai, daga dukkan alamu mahukuntan na Abuja na shirin juyawa kan masana'antu da ragowar talakawa na gari da nufin samar da kusan Naira trilliyan biyu a cikin shidan da gwamnatin take fata ta kashe.

Öl Ölförderung Nigerdelta Niger Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

To sai dai kuma a fadar Aminu Waziri Tambuwal da ke zaman gwamna na Sokoto tuni mahukuntan kasar sun nisa a tunanin nema na ragowar gibin kasafin ba kuma tare da jefa talakawan kasar cikin halin ni 'yasu ba.

"Na farko ta hanyar kafafen samar da abin shiga wanda gwamnatin tarayya ta ke da shi bayan mai sannan kuma gwamnati za karbo bashi domin yi wa al'umma aiki.An kawo maganar yiwuwar kara haraji, amma kuma labaran da muka samu gwamnati ta ce ba za ta kara harajin ba domin zai kuntata wa talakkawa da kuma 'yan kasuwa masu son zuwa saka jari a Najeriya don ci gaban tattalin arzikin Najeriyar"

Kasafin na badi da ke zaman irinsa na farko a kan hanyar cika alkawarin 'yan sauyin har ila yau na zaman zakaran gwajin dafi ga 'yan kasar da ke fata na gani a kasa bayan kaiwa ga kare mulkin 'yan lema na shekaru 16