Tattalin arzikin Jamus ya bunkasa a 2017 | Labarai | DW | 11.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattalin arzikin Jamus ya bunkasa a 2017

Wasu sabbin alkalumman tattalin arziki na kasar Jamus sun bayyana cewa a shekara ta 2017 da ta shude tattalin arzikin kasar ya yi bunkasa da kashi 2,2 cikin dari da ke zama mafi girma a shekaru 27.

Wasu sabbin alkalumman tattalin arziki na kasar Jamus sun bayyana cewa a shekara ta 2017 da ta shude tattalin arzikin kasar ya yi bunkasar da bai taba yin irinta  ba tun bayan fitowar kasar daga masassarar tattalin arzikin da ta fuskanta a shekara ta 2011. 

Sabbin alkalumman sun nunar da cewa tattalin arzikin kasar ta Jamus ya bunkasa da kashi biyu da digo biyu cikin dari a shekarar da ta gabata ta 2017,  wanda ya bai wa kasar damar samun rarar kudi tsaba sama da biliyan 38 na Euro, da ke zama mafi girma da kasar ta samu tun bayan hadewar kasar biyu a wuri daya a shekara ta 1990. 

Wannan na wakana ne duk da tarin kudaden da kasar ta kashe wajen karbar bakin haure sama da miliyan daya a cikin kasar a shekara ta 2016. Sai dai kuma tuni manyan kasashen aminnan kasar ta Jamus musamman na nahiyar Turai, suka soma yin kira ga kasar ta Jamus ta kara ba da himma a fannin cinikayya da su domin taimaka masu ga zaburar da tattalin arzikin kasashen nasu.