Tasirin waƙoƙin addini a Nijar | Zamantakewa | DW | 08.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tasirin waƙoƙin addini a Nijar

A Nijar yau da 'yan shekaru ke nan da al'ummar ƙasar ta shiga wani yanayi na sauraron waƙoƙin addini na yabon manzon Allah aminci Allah da tsira su tabbata a kansa.

Waɗannan ƙasidu na tashen gaske a ƙasar ta Nijar da ma maƙobciyarta Najeriya. Sama da kashi 99 cikin ɗari na al'ummar Nijar ɗin dai musulumi ne.Sha'iran maƙobciyar ƙasar wato Najeriya su ne ke assasa wannan wae da ya zama wata hanya wadda al'ummar musulmi musamman mabiya ɗarikun tasawwufu ke amfani da su a yau wajen ƙwato iyalansu daga sauraron waƙe-waƙen zamani waɗanda ba su dace ba da tarbiyar musulunci ba kamar yadda malam Sani wani tela ya nunar.

Tasirin waɗannan waƙoƙi a kan kafofin yaɗa labarai

Yanzu haka dai gidajen rediyo da talabijin da dama ne su ka ƙaddamar da shiri na gabatar da irin waɗannan waƙoƙi na yabon mazon Allah. Mahamadu fatahu wani sha'iri ne na ƙasar ta Nijar da ke gabatar da wani shiri na waƙoƙin da aka yi wa sunan dausayin Ahlil baiti a wani gidan Rediyo Tenere mai zaman kansa da ke a birnin Yamai, ya ce shirin wani abin alfahari ne.

Ƙalubalen da waƙoƙin yabon ke fuskanta daga jama'a

Yanzu haka musulmai da dama ne ke nuna shakkunsu a kan irin
waɗannan ƙasidu dangane da yadda ake yin amfani da kayan kiɗa abin da suke ganin wani lamari ne da ya shafi bidi'a. To sai dai wani malamin mai yin wa'azi a birnin Yamai malam Naziru Musa ya tabbatar da cewar ƙasidun ba su saɓawa addini ba. Ba shakka waɗannan waƙe dai na zaman wani sauyi na al'adu da ake daf da samu a cikin ƙasashen Najeriya da Nijar inda jama'a ke ta ƙoƙarin faɗikar da iyalensu mahimmanci sauraron waɗannan waƙoƙi fiye da na zamani waɗanda ake dangatawa da kayan shaiɗan.

Mawallafi: Gazali Abdu Tassawa
Edita : Abdourahamane Hassane