1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Matsalar rashin kudi ga FBI

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 23, 2019

Rufe wasu ma'aikatun gwamnati da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta yi a Amirka, ya yi mummunan tasiri ga hukumar binciken manyan laifuka ta Amirkan wato FBI.

https://p.dw.com/p/3C083
Präsident Trump reist für eine Veranstaltung in Utah vom Weißen Haus ab
Präsident Trump reist für eine Veranstaltung in Utah vom Weißen Haus ab
Matakan Trump na shafar fannin tsaro a AmirkaHoto: Getty Images/A. Wong

Rahotanni sun nunar da cewa a yanzu hukumar ta FBI, ba ta iya biyan wasu ma'aikatanta da suka hadar da masu kwarmata mata bayanai da masu yi mata fassara, abin kuma da zai iya shafar yakin da Amirkan ke yi da ta'addanci. Wani jami'in hukumar ta FBI da ya nemi a sakaya sunansa ya nunar da cewa, matsalar na da nasaba da dakile wani bangare na kasasfin kudi da mahukuntan Amirkan suka yi. A ranar Alhamis 24 ga wannan wata na Janairu da muke ciki ne, ake sa ran majalisar dokokin Amirkan za ta tattauna yadda za a kawo karshen rufe wasu ma'aikatun a Amirkan da ya dauki tsahon lokaci. Matakin dai na bukatar amincewar kaso 60 cikin 100 na 'yan majalisar daga bangaren jam'iyya mai mulki ta Republican da kuma ta adawa da ke da rinjaye a majalisar ta Democrats.