Tasirin rikicin Ukraine kan kasuwanci da tattali | Siyasa | DW | 24.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tasirin rikicin Ukraine kan kasuwanci da tattali

Taron kungiyar G7 akan nukiliya da tsaro, zai mayar da hankali kan yadda rikicin na Ukraine zai taimaka wajen kyautata dangantaka tsakanin Amurka da Turai.

Rikicin na Ukraine dama halin da ake ciki bayan Rasha ta mayar da lardin Krimiya a karkashin ikonta, da ci-gaban dandazon sojojin Moscow a kan iyakar kasashen biyu dai, su ne batutuwa da taron yini biyu na kungiyar G7 zai mayar da hankali akai a birnin na The Hague. Bisa dukkan alamu rikicin na Krimiya zai kawo hadin kai da kawancen kasuwanci tsakanin Amurka da kasasahen Turai, daya jima ana kai ruwa rana a kai. Kamar yadda dan majalisar jam'iyyar Republikan na Amurka Charles Dent ya nunar:

Ya ce" a nawa ganin kamata yayi mu yi amfani da wannan damar wajen kirkiro da yarjejeniyar da zata kara hadin kai tsakanin mu Amurkawa da Tarayyar Turai. Domin hakan yana da matukar muhimmanci wajen fadada harkokinmu na tattali a wannan mawuyacin lokaci. Idan muna da kyakkyawar dangantaka a fannin tattali, zai yi tasiri sosai kan matakan tsaro, da zai kara mayar da Putin saniyar ware a fannin tattali."

Putin Russland Sicherheitsrat 21.03.2014

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Tun a shekarar bara ce dai, Amurka da Tarayyar Turai ke tattauna batutuwan da suka danganci rage harajin da kuma cire wasu shingaye a harkokin kasuwancin bangarorin biyu. Manufar hakan dai shi ne cimma nasarar bunkasar tattali a kan mabukatu sama da miliyan 800 da bunkasa rabin tattalin arziki na duniya. Amurka da EU dai na wakiltar kashi daya daga cikin uku na harkokin kasuwanci. Kwararru sun kiyasta cewar cire shinge a harkokin kasuwanci tsakaninsu, zai bunkasa tattalin arzikin nahiyar Turai, sai dai ba zai yi tasiri sosai a bangaren Amurka ba. Sai dai akwai alamun sauyin lamura da sabon rikicin daya ritsa da kasar Ukraine, kamar yadda shima jakadan Jamus a Washington Peter Ammon ya yi amana da shi:

Ya ce " na yi imanin cewar a bayyane take cewar dangantakar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu zai cimma nasara, a wannan yanayi da ake ciki."

To sai ba za'a cimma wannan nasara ba tare da kawar da wasu shingaye da ke kan hanya ba. A 'yan watanni da suka gabata dai an samu karuwar shakku dangane da dangantakar kasuwanci tsakanin Amurka da EU. Akwai zargin rashin fitowa fili da suka, wanda ya jagoranci nuna damuwa a bangaren masu fafutukar kare muhalli da mabukatu da ke nahiyar Turai. Akwai tsoro da sabanin ra'aya dangane da wasu kayayyakin abincin da ake sarrafawa a Amurka. A kan haka ne jakadan Jamus birnin Wasington Ammon ya ce;

" Cimma yarjejeniya tsakanin bangarorion biyu a kan irin wadannan dokoki, ba abu ne mai sauki ba. Hakan na nuni da cewar, ba za mu iya watsi da batuwan da muke da sabanin ra'ayi a kan su kai tsaye ba".

Amurkawan dai sun jaddada bukatar kawar da shinge kan kayayyakinsu na gona, da za'a shigar kasuwannin Turai. Kazalika nan da shekaru shida masu gabatowa, Amurka na muradin maye gurbin yankin Gabas ta Tsakiya a bangaren makamashi. A yanzu haka Amurkan za ta iya jigilar man petur da iskar gas ne kawai, zuwa kasashen da take kasuwanci da su ba tare da shinge ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin