Tasirin kungiyar Obasanjo a siyasar Najeriya | BATUTUWA | DW | 02.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Tasirin kungiyar Obasanjo a siyasar Najeriya

Kungiyar Coalition for Nigeria Movement ta Obasanjo na da burin kwato wa talakawan Najeriya hakkinsu, amma wasu na zarginta da zagon kasa.

Wannan kungiyar da aka kaddamar a birnin Abuja da jihohin Ondo da Ogun a cikin tafiyar da ke da burin sabon sauyi da kuma ke neman kare mulkin APC a badi ta bullo ne kasa da shekara guda da sake zaben shugaban kasa a Najeriya, abin da ke haifar da dumi da zafi a fagen siyasar kasar tsakanin masu neman zarcewa da kuma masu ganin hana wa zarcewar tasiri. 

Injiniya Buba Galadima shi ne shugaban kungiyar reshen Arewa maso Gabashin Najeriya, wanda ke cewa suna da kwarin gwiwar tabbatar da sauyi sakamakon gazawar gwamnatin APC kan wasu alkawuran da ta yi wa talakawa.

Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente (Reuters/Sotunde)

Wasu mata masu zabe a Najeriya

"Manufar kungiyarmu ita ce talaka, ba mu so a zalunceshi saboda da bazarsu ake rawa. Saboda talakawa suke zaban wanda yake mulki."

Daukar umarnin talakawa ko kuma kokarin ci da guminsu, babban fata na kungiyar Coalition for Nigeria Movement dai na zaman amfani da gazawar jam'iyyar APC mai mulki, da nufin tabbatar da sauyin da suke fata su gani cikin kasar. To sai dai Isa Tafida Mafindi da ke zaman jigo a cikin jam'iyyar APC, na ganin yunkurin kafa wannan kungiyar yaudarar talakawa ce.

Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente (Reuters/Sotunde)

'Yan Najeriya a layin zabe a shekarun da suka gabata

"Lokaci ya wuce da za a yaudari dan Najeriya, muna rokon Allah ya kaimu lokacin da za a bukaci kowa ya nuna abin da ya yi a a kasa."

Hukumar zaben Najeriya INEC ta saka watan Fabrairu na shekarar 2019 a matsayin lokacin gudanar da manyan zabukan kasar. Abin jira a gani dai shi ne makomar kungiyar da aka ce ba yanke mata cibiya da nufin muradu na rikidewa zuwa jam'iyyar siyasa ba.

 

Sauti da bidiyo akan labarin