1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina tana kara samun gindin zama a Afirka

Zainab Mohammed Abubakar SB
July 31, 2018

Zaben Mali da Zimbabuwe gami da dangantaka tsakanin Afirka da Chaina suka mamaye sharhin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/32NRg
Senegal Xi Jinping auf Staatsbesuch
Hoto: Reuters/M. McAllister

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta game da ci gaban tasirin kasar Chaina a nahiyar Afirka. Labarin mai taken "Albarka daga kasar Chaina zuwa Afrika ta Kudu", jaridar ta ce tun gabanin taron shugabannin kasashen da tattalin arzikinsu ke yaduwa cikin hanzari  da ake kira BRICS a takaice, Chinar ta yi gagarumar sanarwar zuba jarin makuddan kudade a kasar Afirka ta Kudu mai masaukin baki.

Gipfeltreffen der Brics-Staaten in Südafrika
Hoto: Getty Images/M.Hutchings

Shugaba Xi Jinping na Chaina ya sanar da zuba jari da kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 15 gabannin taron kasashen na BRICS da suka hadar Brazil da Russia da Indiya da China da kuma Afirka da ya gudana a birnin Johannesburg. Daura da haka kamfanonin Afrika ta Kudun da ke durkushewa na samun tallafi daga wannan yakin na Asiya.

Chaina dai ta kafa tarihi a nahiyar Afrika, kasancewar  ta jima ta jima da tasiri ta hanyar zuba jari da kulla yarjeniyoyi na kasuwanci da gwamnatocin kasashe daban-daban. Taron na BRICS dai ya tattauna damar da kasashen ke da su ta hanyar harkokin kasuwanci lokacin da Amirka da Turai suka cimma yarjejeniya kan batun haraji.

Ita kuwa Jaridar Neues Deutschland sharhi ta yi kan zaben kasar Mali. Mai taken "Har yanzu an kasa warware rikicin yankin arewacin Mali" jaridar ta ci gaba da cewar, zaben shugaban kasa karo na biyu, tun bayan juyin mulki a shekara ta 2012. Tun daga shekara ta 2013 ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta girke dakarun kiyaye zaman lafiya na MINUSMA.

Ana iya cewar Mali ta doshi komawa kamar yadda take a baya ke nan? Jaridar ta ce akwai shakku game da hakan. 'Yan takara 24 ne dai ke neman kujerar shugabancin wannan kasa da ke cigaba da fuskantar barazanar 'yan tawaye musamman daga yankin arewaci.

Mali Wahlen
Hoto: Imago/Le Pictorium/N. Remene

Daga cikinsu kuwa akwai shugaba mai ci Ibrahim Boukacar Keita. Sai dai bisa alamu rundunar kiyaye zaman lafiyan na MINUSMA ita ma tana da nata gazawar, na daya dai ta kasa samar da zaman lafiya ba Malin ke bukata. Na biyu sun gaza kare al'umma wanda shi ne makasudun  zamansu a cikin kasar.

Aikin da a hannu guda ya kasance mafi tsada a tahitin ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, wanda ke cin a kalla dala biliyan guda a kowace shekara. Da yawa daga cikin 'yan Mali na cin gajiyar bunkasar tattalin arziki da kasancewarsu a cikin kasar ba wai gwamnati kadai ba. Sai dai abun takaici ne ganin tattalin arzikin kasar na cikin garari sakamakon rashin zaman lafiya.

Simbabwe Präsidentenwahl
Hoto: Reuters/M. Hutchins

Jaridar Die Zeit ta wallafa game da zaben shugaban kasa da a kasar Zimbabuwe. Jaridar ta ce, shekara guda bayan kifar da gwamnatin kama karya, hakan na nufin yanzu dama ce ga al'ummar kasar na gudanar da zabe cikin walwala?

Tsawon shekaru masu yawa Emmerson Mnangagwa ya yi ya na jiran wannan damar. Ya kasance a cikin yamutsi da da siyasar fadar gwamnati na tsawon shekaru 37, ya na fatan rana guda shugaban kasa zai yi murabus shi ma ya samu tasa damar. Hakarsa bata cimma ruwa ba sai a shekarar da ta gabata. Inda bayan kawar da Robert Mugabe mai shekaru 94 da haihuwa Mnangagwa mai shekaru 75 ya haye karagar shugabancin Zimbabwe.

Duniya ta sa ido don ganin zaben wannan zai gudana, inda Nelson Chamisa ke kalubalantar shugaban mai ci a yanzu Emmerson Mnangagwa.