1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

211112 Nigerdelta Öl

February 7, 2013

Duk da rawar da man fetur ke takawa ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya, mazauna yankin da ake hako man na fama da matsalolin rayuwa daban daban.

https://p.dw.com/p/170md
Hoto: Katrin Gänsler

Ba tare da arzikin man fetur ba dai komi zai tsaya cik a Najeriya domin kuwa tana samun kimanin kaso 80 cikin 100 na kudaden shigar ta ne daga man fetur, wanda kasar ta gano tun cikin shekara ta 1958, kuma ya sanya ta a matsayi na akwas cikin jerin kasashen da ke samar da mai a duniya baki daya. Sai dai kuma maimakon haka ya zama alheri ga mazauna yankunan da ake hako man fetur din, sai ga shi suna cikin mummunan yanayi na rayuwa sakamakon gurbacewar muhalli da shakar iska mai gubar da ke fitowa a lokacin samar da mai.

Yankin Neija Delta da ke tarayyar Najeriya dai na zaman yankin da ke samar da albarkatun man fetur da kasar ke tinkaho da shi wajen samun kudaden shiga. Sai ai kuma al'ummar yankin na fama da matsalolin da suka hada da gurbatar ruwan da ke yankunan su sakamakon ayyukan hako albarkatun man fetur:

Wannan wani kwale-kwale mai inji ne ke zirga - zirga a kauyen Bodo da ke yankin Neija Delta - mai arzikin man fetur a Najeriya, wanda kuma ke matsayin babbar hanyar sufuri ga dubbannin jaa'ar da ke rayuwa a kauyukan da ke yankin.

Ko da shike mazauna kauyen Bodo sun shafe shekaru da dama suna dogara akan kamun kifi domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, amma wannan yanayin ya sauya tun a shekara ta 2008, bayan malalar man fetur zuwa cikin wuraren da suke kamun kifin na tsawon makonni.

Afrikas Rohstoffe - Was bleibt vom Boom
Joshua na daya daga cikin masu kona mai a YenagoaHoto: Katrin Gänsler

Kamun kifi ne sana'ar al'ummar Bodo

Shekaru hudu bayan fashewar bututun daya janyo matsalar, kanfanin hako fetur na Shell da ke da alhakin kula da bututun, bai dauki wani matakin a zo a ganmi ba, abinda yasa ha yanzu mutum zai iya ganin ta'adin da malalar ta janyo, kuma a cewar Saint Emmah Pii, wani mazaunin yankin halin da suke ciki abin takaici ne :

"Ga shi dai kana ganin abinda ya saura daga gurbataccen man fetur daya malala zuwa cikin ruwan. Babu wani abu mai rai daya saura cikin sa. Ina tabbatar maka da cewar gabannin malalar man fetur a nan, mutane manya da kanana na zuwa nan domin kamun kifi da kuma kaguwa. Kai! Akwai abubuwa da dama kuma harkar tattalin arziki na bunkasa a wannan yankin kafin matsalar." 

Saint Emmah Pii da ke shugabantar kungiyar al'ummar Bodo, ya ce akwai alkaluma mabanbanta dangane da yawan man fetur daya malala zuwa cikin tekun, a tsawon makonnni 10 da matsalar ta afku. Yayin da kanfanin Shell ke cewar kimanin ganga dubu 4 ne, ita kuwa kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International cewa take yawan man fetur daya malala zai kai ganga dubu 311.

Sai dai matsalar malalar gurbataccen man fetur ba ta tsaya ga yiwa masunta kawai mummunar illa ba. su ma manoma ta yi matukar shafarsu:

DW_Delta-online3
Hoto: Katrin Gänsler

Malalar man fetur na yin mummunan tasiri ga Neija Delta

Faranziska Zabbey, da ke zama daya daga cikin matan da malalar man fetur a yankin Bodo ta janyowa cikas ga samun abinci dai ta tuna bara, wanda ke nuna cewar ba ta ji dadin bana ba:

"Ta ce bayan gurbata muhallin da man fetur ya janyo, ba ma iya zuwa yankunan da muke tsintar 'ya'yan itatuwa ko kuma gona. Ina kira ga kanfanin Shell daya taimaka mana domin kuwa mun rasa hanyar samun kudin shiga saboda matsaolin da man fetur ya janyo mana."

A lokacin da Najeriya ta gano cewar tana da albarkatun man fetur a shekarun 1950 dai, ta kyautata zaton samun ingantacciyar makoma ta fannin bunkasa, yayin da al'ummar yankin Neija Delta kuwa suka amince da alkawarin samun kyakkyawar rayuwa da ci gaba, amma kuma bayan fara hako man fetur din a shekara ta 1958, ba haka lamarin ya kasance ba. Innocent Masi, wani Likitan daya yi ritaya daga yankin, wanda kuma ke zaune a kauyen Omoku da ke kusa da birnin Fatakwol, ya ce al'amarin yana da ban takaici:

"Abubuwa sun sauya sosai, domin kuwa a shekara ta 1962 lokacin da manyan kanfanonin man fetur suka fara zuwa ne na je makamarantar sakandare, amma bayan kammala jami'a kuma na dawo nan a shekara ta 1976, na fahimci cewar abubuwa sun yi tsanani sosai, kuma na ga sauye sauye da dama."

Wasu daga cikin matsalolin da Innocent Masi, kwararren likitan da ya yi ritayar ya lura da su dai sun hada da illar da ayyukan kanfanonin hako man fetur ke janyowa ga rayuwar al'umma sakamakon gurbatacciyar iskarr gas da suke fitarwa, inda ma Najeriya ke matsayi na biyu baya ga Rasha a duk fadin duniya wajen fitar da iskar Gas:

"Akwai mutane da dama da ke fama da matsalolin da suka shafi cututtukan fata. Mata da dama na fama da rashin haihuwa - idan ka kwatanta da wasu wurare. Hayakin na lalata rufin gidaje, domin kuwa cikin dan karamin lokaci sai su fara yoyo. Wadannan na daga cikin matsalolin da na lura."

Ayyukan kanfanonin mai na taimaka wa sauyin yanayi 

Gurbatacciyar iskar Gas dai matsala ce da manyan kanfanonin man fetur na kasa da kasa irin su Shell ke dari-dari wajen daukar matakan shawo kansu. Kanfanin Shell na sahun farko cikin jerin manyan kanfanonin da ke taka rawa cikin harkar ma'adinai da iskar Gas, kuma kanfanin ya yi tsawon shekaru 50 yana gudanar da harkokinsa a Najeriya. Philip Mshelbila, darektan kula da sha'anin bunkasa da kuma dangantaka da al'umma a kanfanin, ya kare kanfanin bisa zargin yin hubbasa ta wannan fannin:

Titel: DW_Delta-online1
Hoto: Katrin Gänsler

"A ganina ana ruruta irin illar da iskar Gas ke janyowa ga lafiyar jama'a, kuma ina batu ne akan kiwon lafiya, domin kuwa akwai illar da ta shafi muhalli da kuma yanayi. Amma muna mayar da hankali neakan hanyoyin da za mu inganta sha'anin kula da lafiyar jama'a da kuma ci gaban rayuwarsu. Iskar gas da ke gurbata yanayi, batu ne da muka daukar tsauraran matakan shawo kan matsalar."

Sai dai kuma ana sa ran nan da shekara ta 2013 Najeriya za ta shawo kan matsalolin da suka shafi batun iskar Gas da ke gurbata yanayi saboda kudirin dokar da ta shafi sha'anin man fetur, da ke gaban majalisar dokokin kasar ya tabo wannan matsalar, abinda kuma ake ganin idan har ya zama doka, to, kuwa za ta yi kyakkyawan tasiri ga rayuwar al'ummar yankin Neija Delta, amma gabannin zartar da dokar, Philip Mshelbila na kanfanin Shell, ya ce suna yin namijin kokarin daya kamata a yaba musu:

"Muna la'akari da cewar ayyukan da muke gudanarwa na shafar mazauna yankuna da kuma wuraren da muke yin ayyukan. A bisa wannan dalili ne muke gudanar da manyan ayyukan da za su rage mummunan tasirin da ayyukan mu na hako man fetur da kuma iskar Gas ke janyowa da kuma bada fifiko ga ayyukan bunkasa rayuwar al'ummomin yankunan da muke yin ayyukan."

Matakan warware matsalolin da yankin Neija ke fama dasu

Ayyukan da jami'in na kanfanin Shell ke yin tsokaci akai dai na cikin jerin yarjejeniyar fahimtar junan da kanfanin ya sanyawa hannu akai are da al'ummomin yankin, wadda a karkashinta ne kuma kanfanin ke tallafawa gyara makarantu da samar da su da kuma kananan asibitoci da dai sauransu - ciki kuwa harda asibitin Obio Cottage Hospital da ke birnin Fatakwol, wanda ke yin gwaji tare da baiwa mata masu juna biyu da ke fama da cutar AIDS maganmi kyauta, - asibitin da kuma ke da kwararrun likitoci, harma ke shan yabo ga marasa lafiya irin Onyinye Ben:

DW_Delta-online4
Juliette na neman karanzir ta saya a YenagoaHoto: Katrin Gänsler

"Suna yin kokari, kuma kanfanin Shell ne ke kawo magungunan daga ketare. Ina sha'awar yanda suke tarbar marar lafiya kuma zan bada shawarar zuwa gareshi. Wannan shi ne asibitin daya fi kyau anan."

Sai dai duk da irin wadannan ayyukan za'a iya cewar da sauran jan aiki a gaba domin kuwa hatta a baya bayannan hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin ta yi gargadi game da karuwar jama'a da ke samun kansu cikin mummunan yanayin rayuwa a yankin Obodo daya hada da Ogoni da ma daukacin yankin, muddin dai gwamnatin Najeriya da manyan kanfanoni basu yi wani tanadi ba.

Wani abin farin ciki ga al'ummar, wadda tare da taimakon lauyoyi suka shigar da kara a birnin the Hague dai shi ne cewar akwai yiwuwar su sami diyya daga kanfanin Shell bisa lala'ta musu muhalli.

Infografik Öl-Exporte in Nigeria 2010 HAU Hausa
Yawan man fetir da Najeria ta sayar a 2010

Mawallafa : Katrin Gänsler / Saleh Umar Saleh
Edita        : Mohammad Nasiru Awal