1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

050611 Wirtschaftsfaktor Frauenfußball

June 24, 2011

An sha ɗoki da murna dangane da gasar ƙwallon ƙafa ta ci kofin duniya da aka gudanar a Jamus a shekara ta 2006.

https://p.dw.com/p/11j6R
Hoto: picture alliance/augenklick

To sai dai kuma babu wani mizanin da aka bayar dangane da rawar da gasar taka ga tattalin arziƙin ƙasar. Bisa ga dukkan alamu kuwa haka lamarin zai kasance dangane da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ta mata a ƙasar daga 26 ga watan Yuni zuwa 17 ga watan Yuli.

Yau dai kimanin shekaru biyar ke nan suka shuɗe tun bayan kammala gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ta maza da aka gudanar a nan Jamus. Dubban ɗaruruwan masu sha'awar ƙwallon ƙafa suka shigo ƙasar daga ƙasashe daban-daban na duniya domin a dama da su a shagulgulan wasannin. Dangane da gasar ta mata kuwa a bana, lamarin ya danganta ne da irin ƙwazon da 'yan wasan zasu nunar da kuma yadda yanayi zai kasance, wanda ba wanda zai iya yin tasirin kansa. Dangane da tasirin gasar akan tattalin arziƙin ƙasar ta Jamus kuwa, ba a sa ran cewar gasar zata haifar da wata bunƙasa ta a zo a gani. Henning Vöpel masanin tattalin arziƙi ne dake shugabantar sashen "Wasanni da tattalin arziki" a cibiyar nazarin al'amuran tattalin arzikin duniya dake birnin Hamburg. Bisa saɓanin yadda al'amura suka kasance dangane da gasar cin kofin duniya ta maza shekaru biyar da suka wuce, bisa ga ra'ayinsa, babu wani tasiri na a zo a gani da gasar ta mata zata yi:

"Shagulgulan gasar ƙwallon ƙafa cin kofin duniyar ta mata ba zasu kai su dawo ba. A saboda haka bai zama abin mamaki ba kasancewar gasar ba zata yi wani tasiri na a zo a gani ga tattalin arzikin ƙasa ba. Da wuya mutane su canza wani salo na rayuwarsu ta yau da kullum. Masu fita zuwa ƙasashen ƙetare don hutu zasu yi tafiyarsu bisa saɓanin yadda lamarin ya kasance dangane da gasar cin kofin duniyar ta maza."

To sai dai kuma ko da yake ba a sa ran cin gajiyar gasar ta mata a fannin tattalin arziƙi da kuma ƙarancin 'yan kallo, amma fa bai kamata a rena muhimmancin wasan ga masu ɗaukar nauyinsa ba. Domin kuwa gasar ta mata tana da wata muhimmiyar rawar da take takawa a al'amuran tallace-tallace.

Mawallafa: Dirk Kaufmann / Ahmadu Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal