Tasirin abinci mai gina jiki ga yara | Zamantakewa | DW | 03.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tasirin abinci mai gina jiki ga yara

Ƙalubale na wayar da kan al'ummomin Arewacin Najeriya a kan inganta samar da abinci mai gina jiki ga yara da kuma magance cututtuka da ke addabar yara ƙanana.

Kowace Al'umma da ke son ganin ta ci gaba da bunƙasa da kuma yin fice a cikin sauran ƙasashen duniya dolle ne ta tabbata, yara manyan gobe da zasu taso daga baya sun samu ababben da suka dace don ba su damar girma da hazaka wajen tafiyar da kasarsu. Wannan kuma na somawa ne tun lokacin raino yara ƙanana bayan haifuwa.

Rashin faɗikar da al'umma na zaman dalili na farko na jahiltar ciyar da yara abincin

Matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da kuma cututtuka da ke addabar rayuwar yara ƙanana sune matakai na farko da ya kamata a magance don cimma wannan ɓuri a shekaru nan gaba.Ƙarancin faɗakarwa da kuma illmantar da iyalai a kan abinci mai gina jiki da alluran riga kafi shi ne hukumomi irin su UNICEP suka nemo hanyar cike giɓin ta amfani da kafaffen yaɗa labarai da jama'a ke kallo ko saurare a kullun kamar yadda Malam Rabiu Musa na UNICEP ke cewa: ''Kafafen yaɗa labarai na iya ƙoƙarin faɗakar da jama'a a kan yadda iyalai za su inganta lafiyar yara wajen samar da abinci mai gina jiki kuma aiki ne da suka jima suna yi,kuma dolle kafafen su inganta fadakarwar don cimma ɓurin.''

Ƙoƙarin mata na samar da ingantaccen abinci ga yara

Mata ma a matsayin iyaye da suka san irin yadda jamaa ke fama da karancin ilmi na yanda zasu samar da abinci mai gina jiki ga yaransu da kankanin abin da suke da shi, shine zai ɗauki hankalin. Sau da yawa ne kafafen yaɗa labarai ke ƙoƙarin faɗakar da jama'a a kan irin waɗannan ababben. Yanzu dai aiki na kara faɗaɗɗa faɗakarwar ga jama'a a kan yadda za su inganta abinci mai gina jiki da kuma ba da damar yi wa yara Alluran riga kafi aiki ne da kafafen yada labarai za su mayar da hankali akai kamar shan ruwa, domin taimakawa yaran wannan yankin na arewacin Najeriya daga fadawa kamuwa da cututtuka da kuma yunwa.

Mawallafi : Aminu Abdullahi
Edita : Abdourahamane Hassane