1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin masallacin Kudus ya dauki hankalin duniya

Mahmud Yaya Azare
May 10, 2021

Kungiyar kasashen Larabawa ta nuna fushi tare da kiran Israila ta dakatar da dukkan tsokana ga masu ibada a masallacin Kudus mai daraja.

https://p.dw.com/p/3tDFv
TABLEAU | Israel Jerusalem | Spannungen & Gewalt
Hoto: Ahmad Gharabli/AFP/Getty Images

Magatakardar kungiyar kasashen larabawa Ahmad Geit wanda ya yi Allah wadai da matakin amfani da karfi akan masu Ibada a masallacin Kudus ya bukaci Israila ta dakatar da dukkan wata tsokana da za ta iya haifar da damuwa.

"Birnin Kudus     jan layi ne da ba za mu taba lamunta a tsallaka shi ba. Hana masu ibada gudanar da ayyukan ibadarsu da keta hurumin masallacin Al-aqsa mai daraja da Yahudawa masu tsautsauran ra'ayi ke yi, wadanda jami'an tsaron Isra'ila ke yi, wannan yunkurin ta da yakin addini ne da ya zama wajibi kasashen duniya su yi Allah wadai da shi, su kuma tabbatar da ganin an kawo karshensa domin ba musulmin da zai lamunta da keta hurumin masallacin Al-aqsa  mai alfarma.

Israel Palästina | Raketen werden vom Gazastreifen nach Israel abgefeuert
Harin rokoki daga GazaHoto: Mohammed Salem/REUTERS

Rikicin da ke zama mafi muni a cikin 'yan shekaru da suka gabata, ya raunata sama da Falasdinawa 200 da 'yan sandan Isra'ila akalla 17 kamar yadda ma'aikatan lafiya da 'yan sandan Isra'ila suka bayyana, bayan da 'yan sandan Isra'ila   suka hana gomman motocin safa-safa da ke dauke da Musulmi da ke zuwa Masallacin na kudus domin ibada wucewa. Tun da farko sai da jami'an tsaron na Israila suka yi dirar mikiya kan wata unguwa a birnin na Kudus, dama kuma sun kama Falasdinawa da yawa kan rikicin korar Falalsdinawa daga gidajensu,don bawa Yahudawa 'yan kama wuri zauna a birnin.

Firaim ministan Isra'ila Benjamin Netenyahu, a wannanLitinin din, ranar da Isra'ilan ke bikin tunawa da ranar da suka kwace birnin na Kudus daga Falalsdinawa a shekarar 1967 yace, babu gudu babu ja da baya a matakin da gwamnatinsa ke dauka na tabbatar da ikonta a birnin Kudus da yake siffantashi da fadar mulkin kasar Isra'ila. 
Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi sun lashi takobin kutsawa cikin Masallacin na Al-Aqsa,wanda suke ikirarin cewa, an gina shi ne a gurbin babban wurin bautar Yahudawa da ya zama wajibi a rusa masallacin don sake gina wurin bautarsu.

Israel | Unruhen in Jerusalem
Dauki ba dadi a birnin KudusHoto: Mahmoud Illean/AP Photo/picture alliance

Shugaban Hukumar Falalsdinawa Mahmud Abbas ya nemi kasashen duniya da su kawo wa Falalsdinawan dauki don ceton su daga wadanda ya kira masu mulkin wariya 'yan mamaya dake neman jirkita tarihi karfi da yaji saboda goyan bayan da Amurka ke basu.

A yayin da kungiyar Hamas ta harba gomman rokoki kan yankunan mamayar Isra'lia na Falasdinawa matakin da ta ce alama ce ta tabbatar da cewa tana nan kan bakarta na 'yanta yankunansu ko ana ha maza ha mata.