Tashin hankali ya hallaka mutane 10 a Ukraine | Labarai | DW | 01.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin hankali ya hallaka mutane 10 a Ukraine

Ukraine tana ci gaba da fuskantar tash-tashen hankula a yankin gabashin kasar

A wannan Laraba sabon tashin hankali ya yi sanadiyar hallaka mutane 10 a garin Donetsk na gabashin kasar Ukraine, da suka hada da malaman marakanta da dalibai.

Tashin hankalin ya barke ranar da ake komawa makarantu inda a watan jiya aka kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan aware. Tuni Amirka ta nuna damuwa bisa tashin hankalin da ake ci gaba da samu a kasar ta Ukraine, yayin da kungiyar Tarayyar Turai ta amince da ci gaba da aiki da takunkumi kan mahukuntan Rasha da ake zargi suna ingiza wutar rikicin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane