tashin hankali ya barke a Kinshasa gabanin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 11.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

tashin hankali ya barke a Kinshasa gabanin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa

An yi arangama tsakanin magoya bayan shugaban JDK Josef Kabila da mataimakin sa kuma babban dan hamayar sa Jean Pierre Bemba a Kinshasa babban birnin kasar. Jami´an sa ido na MDD a Kinshasa sun ce an yi harbe harbe to amma kawo yanzu ba wani karin bayani game da asarar rayuka. Tashin hankali ya barke ne a lokacin da ´yan Kongo ke zaman jirar sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 29 ga watan oktoba, inda aka yi takara tsakanin Kabila da Bemba. Ana sa ran samun sakamakon karshe na zaben daga yanzu zuwa ranar 19 ga watannan na nuwamba. Alkalumma sun yi nuni da cewa Kabila ke kan gaba a yawan kuri´u inda ya samu kashi 60 cikin 100 musamman daga gabashin kasar.Rahotanni daga Kinshasa sun ce magoya bayan Bemba sun kakkafa shingaye a kan tituna dake unguwar da yake da zama kana kuma sun yi ta cunnawa tayoyi wuta.