1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin bama-bamai da musayar wuta a Maiduguri da Damaturu

December 23, 2011

Aƙalla mutane shida sun rasu a tashin-tashina da suka auku a birane uku dake arewa maso gabacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/13YZI
epa02994304 A burned out security vehicle on a road following a bomb blast in Damaturu northern Nigeria 06 November 2011. Attacks over night on 04 November have claimed the lives of over 60 people in northern Nigeria according to reports from the Red Cross. Hundreds have been reported to have fled towns as churches and police have been targetted. The Islamist militant group Boko Haram has claimed responsibility for the attacks. EPA/STR
Hoto: picture-alliance/dpa

Tashe tashen hankula a birane uku dake arewa maso gabacin Najeriya sun yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane shida, bayan musayar wutar manyan bindigogi da fashe fashen bama-bamai sun addabi yankin dake fama da rigingimu. Tashe tashen hankulan sun ɓarke ne a biranen Maiduguri, Damaturu da kuma Potiskum da yammacin ranar Alhamis. An kuma jin ƙarar harbe harben bindiga a Damaturu a wannan Juma'ar, sai dai babu ƙarin bayani. Amma wata majiyar asibiti a Damatutu ta ce an kashe soja ɗaya da raunata 'yan sanda shida sai kuma wani yaro ɗan shekara 10 da aka yi wa aikin tiyata bayan an harbe shi da bindiga. A Potiskum rahotannin sun ce mutane biyar ne suka rasu. An kuma yi ƙone ƙone, musamman motocin 'yan sanda.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi