Tashin bam ya hallaka mutane 20 a Gombe | Labarai | DW | 22.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bam ya hallaka mutane 20 a Gombe

Kimanin mutane 20 ne aka bada labarin rasuwarsu bayan da wani bam ya fashe a tashar Dukku da ke garin Gombe a arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.

Masu aiko da rahotanni suka ce bam din ya tashi ne da karfe goma da rabi na safiyar wannan Litinin din kuma galibin wanda suka rasu din matafiya. Tuni dai jami'an tsaro da kungiyoyin bada agaji suka killace wajen kana aka garzaya da wadanda suka jikkata asibitoci da ke garin don samun magani.

Tasahar ta Dukku dai na daga cikin tashoshin da ke samun cinkoson mutane sakamakon irin motocin da ake samu zuwa garuruwa da dama a cikin jihar da ma jihohin da ke makotaka da ita.Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dau alhakin kai wannan harin da ma dalilin yin hakan. A 'yan watannin dai jihar Gombe na fuskantar hare-hare na 'yan kunar bakin wake da kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai.