Tashe-tashen hankulla a Irak | Labarai | DW | 04.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe-tashen hankulla a Irak

Kwana ɗaya bayan harin ta´adancin da ya hadasa mutuwar mutane fiye da 130 a ƙasar Irak,gwamanti ta jaddada aniyar yaƙar yan ta´ada ba ji ba gani.

Wannan shine hari mafi muni, da ya wakana a ƙasar, tun bayan kiffar da tsofan shugaban ƙasa, mirgayni Saddam Hussain, a shekara ta 2003.

Saidai a wani abu mai kamada a na magani kai na kaba, jim kaɗan bayan wannan sanarwa, yan ƙunar baƙin wake, sun kai wani saban hari a birnin Bagadaza, da sanhinsahiyar yau lahadi,wanda ya ɗauki rayukan mutane 15.

A nata ɓangare, rundunar Amurika a Irak, ta bayyana ƙarin mutuwar sojojinta 2, a filin daga.

A cikin wata sanarwar da ta hiddo, ƙunguiyar gamayya turai ta yi Allah wadai, da taɓarɓarewar al´ammuran tsaro a Irak, ta kuma yi kira ga ɓangrorin da abun ya shafa, su duƙufa wajen kawo ƙarshen wannan masifa.