Tashe-tashen hankulla a ƙasar Iraƙi | Labarai | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe-tashen hankulla a ƙasar Iraƙi

A ƙasar Iraƙi a na ci gaba, da yaƙe yaƙe tsakanin yan sunni da yan chi´a, a sakamakon harin da wasu mutane, da ba a tantance ba, su ka kai ga ɗaya ,daga mahimman wuraren ibadar yan chi´a.

A sahiyar yau rahotani daga assibitocin ƙasar sun ce an ƙara kai gawwawakin wasu mutane 80.

A baki ɗaya, mutane 130 su ka rasa rayuka, tsakain jiya laraba zuwa yau.

A birane daban daban, da su ka haɗa da Bakuba Bassorah da Bagdaza, yan chi´a na kai hare haren ramuwar gayya ga massalatan yan sunni, da su ke zargi da ruguza wurin ibadar na su.

A sahiyar yau, shugabanin ɗarikar sunni, sun tuhumi jagoran yan Chi´a, Ayatollah Ali Sistani,da ƙara rura wutar wannan rikici.

Kazalika, sun ƙauracewa taron da gwamnati ta kira, tsakanin bangarorin 2, domin maido da zaman lahia.

Gwamnati, ta kafa dokar hanna hitar dare, daga ƙarfe 8 har zuwa 6 na sahe.

Yau ne, dokar zata fara aiki , bugu da ƙari, an ƙarfafa mattakan tsaro a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Wannan sabin tashe tashen hankulla da su ɓarke a ƙasar Iraƙi sun rutsa da ma´aikata 3 na gidan Talbajan Al Arabiya da su ka rasa rayuka.