Tashe-tashen hankula na ci gaba a Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 25.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Tashe-tashen hankula na ci gaba a Afirka

Rikicin Boko Haram a Najeriya da yakin basasan da ya ki ya ki cinyewa a Sudan ta Kudu na daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin jaridun na Jamus.

"Tun lokacin da gwamnatin Najeriya ta kaddamar da yaki a kan Boko Haram. kungiyar ke kara yin karfi maimakon ta yi rauni. A wannan makon ma tashin bama-bamai suka mamaye rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, musamman tagwayen hare-hare bam da suka girgiza garin Kaduna a ranar Laraba. A farkon mako shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da iyaye da kuma wasu 'yan mata 'yan makarantar Chibok da suka kubuta daga hannun Boko Haram, ana dab da cika kwanaki 100 da sace 'yan matan daga makarantarsu kuma har yanzu shiru ka ke ji kamar an aiki bawa garinsu. A farkon makon kuma sojojin Najeriya sun samu koma-baya bayan da Boko Haram ta karbi iko da garin Damboa inda rahotanni suka ce ta kafa tutarta a garin. Najeriya da ta fi yawan al'umma a jerin kasashen nahiyar Afirka da kuma ke da karfin tattalin arziki albarkacin man fetir, kuma ke zama wata cibiyar raya al'adu, amma galabar da Boko Haram ke samu na zama abin damuwa ga kasashe makwabtanta, da su ma ke da na su matsalolin da masu kaifin kishin addini."

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Sudan ta Kudu ne inda a nan ma ake fama da wani tashin hankalin.

Yakin basasa a Sudan ta Kudu

Ta ce: "Wani fada mafi muni a cikin watanni uku ya dakushe duk wani fatan samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu. Mutane da yawa aka kashe sannan da dama suka tsere a wani bata-kashi tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye, wadanda suka yi ikirarin kame birnin Nazir, shalkwatar lardin arewacin kasar. Su ma dakarun gwamnati sun mayar da martani. Majiyoyi masu nasaba da magoya bayan gwamnatin Sudan ta Kudu sun ce 'yan tawaye sun rasa daruruwan sojoji ciki har da yara da ake tilasta musu daukar makami. Ita ma tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudun ta tabbatar da gumurzun wanda ta ce shi ne mafi muni a kasar tun bayan fara tattauna batun wanzar da zaman lafiya tsakanin marikitan."

Wa zai fi amfana da yarjejeniyar EPA?

Har yanzu dai jaridar ta Die Tageszeitung ce ta rawaito mana cewa hukumar kungiyar tarayyar Turai da wasu kasashe shida na yankin kudancin Afirka sun amince da wata yarjejeniyar ciniki. To sai dai har yanzu ba a bayyana ka'idojin yarjejeniyar ba wadda ke karkashin yarjejeniyar ta tattalin arziki tsakanin Afirka da EU wato European Partnership agreement. Hukumar ta EU ta ce ta cimma yarjejeniyar ce da kasashen Botswana, Lesotho, Mozambik, Namibiya, Afirka ta Kudu da kuma Swatziland. Ta kwatanta yarjejeniyar da wani makamin samun ci gaba, kirkiro da aikin yi da kuma bunkasar arziki. To sai dai masu adawa da yarjejeniyar sun yi Allah wadai da ita suna masu cewa za ta ba wa kasashen Turai izinin jibge kayakin amfanin gonarsu a Afirka wanda zai kassara manoman wannan nahiya, da a dama ke fama da matsaloli saboda karya farashin kaya da Turan ke yi saboda tallafin da take ba wa manomanta."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu