Tashe tashen hankula a Iraki a rana ta farko ta azumin ramadana | Labarai | DW | 23.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Iraki a rana ta farko ta azumin ramadana

A rana ta farko da fara azumin watan ramadana an kai wani mummunan harin bam a unguwar Sadr City ta ´yan shi´a dake wajen birnin Bagadaza. Akalla mutane 34 suka rasu sannan fiye da 30 suka samu raunuka a fashewar wani bam da aka dana cikin mota a kusa da wani gidan mai. Wata kungiya da ta kira kanta jama´atul Jundal Sahaba ta yi ikirarin kai harin. Rundunar sojin Iraqi ta yi gargadi game da karuwar kai hare hare a Iraqi cikin watan azumin na ramadana. A kuma can garin Muktadiya dake arewa da birnin Bagadaza, jami´an tsaro sun kame madugun kungiyar Ansar al-Sunna, da ake zargi da kai hare haren ta´addanci a fadin kasar Iraqi.