Tashe-tashen hankula a Burundi | NRS-Import | DW | 06.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Tashe-tashen hankula a Burundi

Wannan yana cikin kalaman da ƙungiyar kula da rikice-rikice ta Crisis Group mai mazauni a birnin Brussels na ƙasar Beljiun ta bayyana.

Wannan yana cikin kalaman da ƙungiyar kula da rikice-rikice ta Crisis Group mai mazauni a birnin Brussels na ƙasar Beljiun ta fitar a cikin rahoton wannan Alhamis da ta gabata. Tashe-tashen hankulan sun ta'azzara tun lokacin da Shugaba Pierre Nkrunziza ya yi tazarce karo na uku da ya saɓa kundin tsarin mulki.

Brazanar tashe-tashen hankula na ƙaruwa a duk faɗin ƙasar ta Burundi

Amma wani abin da ya janyo lamura suka sukurkuce a cewar Comfort Ero ke zama daraktar kungiyar ta Crisis Group mai kula da nahiyar Afirka shi ne rashin tattaunawa."Ina tsammani ana sane da cewar kafin yanzu Burundi ta kama hanyar samun yaƙin basasa kamar wanda aka gani a shekarun 1990. Muna damuwa da halin da ake ciki , musamman daga shugaban majalisar dattawa gami da wa'adin mai haɗari da shugaban ƙasar ya bayar."

Babban cikas shi ne rashin tattaunwa tsakanin 'yan siyasa na ƙasar

Shi dai shugaban majalisar dattawa ta Burundi Reverien Ndikuriyo ya yi gargaɗin cewar nan da lokaci ƙanƙani 'yan sanda za su fara aiki, kuma ya nemi jami'an yankuna su yi fito na fito fda waɗanda suke yin kunnen ƙashi da dokoki, abin da ake gani suna kama da kalaman da aka yi amfani da su lokacin kisan ƙare dare dangin Ruwanda a shekarun 1990. Sannan Comfort ta ƙara da cewar ''Ina tsamanin yana da haɗari saboda ya yi kama da abin da ya faru a shekarun 1990, babu niyar shiga tattaunawa, yana ƙara tsaurara ra'ayi, kuma tun watan Afrilu ba ya sauraron muryoyi a ciki da waje waɗanda suke kira kan sasantawa."

Ranar Litinin mai zuwa Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya zai tattauna kan rikivcin na Burundi.Ma'aikatar harkokin wajen Jamus tana cikin waɗanda suka nuna damuwa bisa abin da ke faruwa a Burundi.

Sauti da bidiyo akan labarin