Tashar DW ta soki mahukuntan Turkiya | Labarai | DW | 06.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashar DW ta soki mahukuntan Turkiya

Shugaban tashar DW Peter Limbourg ya bayyana a shafin tashar na Internet cewa abin da mahukuntan kasar Turkiya ke yi, ya sabawa ka'idojin dimokradiya.

Shugaban tashar DW Peter Limbourg

Shugaban tashar DW Peter Limbourg

Kafar yada labari ta talabijin da rediyo ta DW ta yi kakkausar suka bayan da aka kwace kayan aiki na ma'aikatanta biyu da suka nadi tattaunawa da minista a kasar Turkiya, abin da kafar yada labaran ta bayyana da wani mataki na hana 'yancin fadar albarkacin baki.Shugaban tashar ta DW Peter Limbourg ne ya bayyana hakan a shafin tashar na Internet yana mai cewa abin da mahukuntan kasar ta Turkiya ke yi ya sabawa ka'idojin dimokradiya.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai aka yi wata tattaunawa da ministan matasa da wasanni na Turkiya Akif Caoatay Kilic wanda cikin tambayoyin da 'yan jaridar na DW suka yi masa sun hadar da batun yunkurin juyin mulki da ya gaza nasara da abin da ya biyo baya da ma tattaunawa kan kare hakkin mata. Da kammala wannan tattaunawa dai a ofishin ministan da ke a birnin Ankara, ministan ya sauya shawara inda anan ne ma'aikatansa suka kwace na'urorin da suka nadi bidiyon wannan tattaunawa. Duk kuma kiran da DW ta yi na ya dawo da su ya yi kememe.