Tarwatsewar Bomb a Qalat,Afganistan ya raunana mutum guda | Labarai | DW | 14.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarwatsewar Bomb a Qalat,Afganistan ya raunana mutum guda

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bomb daya dauke dasu,adaidai lokacin da ayarin motocin yan kwanli na kasashen ketre ke wucewa ,saidai harin bai kashe kowa ba bayan mutum guda daya jikkata a Afganistan da safiyar yau.Sai daio rahotanni dake fitowa daga birnin Kandahar dake kudancin kasar dai na nuni dacewa ,dan kunar bakin waken ya mutu nan take.Jamiin yansanda Mohammad Asif ya fadawa manema labaru cewa,babu wanda ya jikkata baya ga wani farin hula daya,sai dai gabubbukan jikin dan kunar bakin waken ya tarwatse.Mr Asif yace wadannan yan kwangila na soji suna aiki ne wa wata masanaantar gine gine ta Amurka,wadda ke aikin ginin gadar sansannin dakarun soji dake garin Qalat,wanda ke gunduwar Zabul a kudancin wannan kasa ta Afganistan dake cigaba da fuskantar barazanar yan yakin sunkuru.