Taron yanayi da riga kafin yake yake a Afrika na birnin Arusha a Tanzania | Labarai | DW | 05.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron yanayi da riga kafin yake yake a Afrika na birnin Arusha a Tanzania

default

A birni Arusha na kasar Tanzania, yau ne massana ta fannin yanayi da gandun daji, daga kasashe kimanin 20 na Afrika, su ka buda zaman taro.

A tsawan kwanaki 4 mahalarta wannan taro za su masanyar ra´yoyi, a game da alakar da ke akwai, tsakain albarkatun ruwa namu, da gandun daji, da kuma yawan yake yake, da ke rikirkita Afrika.

Cibiyar riga kafi da hana yaduwar yake yake ta kasar jamus ta shirya wannan zaman taro.

Za a shirya makamancixyar wannan haduiwa a sati mai zuwa a kasar China tare da kasashen kudu maso gabbacin Asia.

Baban burin da ake bukatar cimma shi ne na rage yawan yake yaken bassasa a wannan yankuna na Afrika da Asia.