Taron tattalin arziki na duniya ya kawo sauye-sauye | Zamantakewa | DW | 24.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taron tattalin arziki na duniya ya kawo sauye-sauye

Taron tattalin arziki na duniya da aka gudanar a birnin Davos na Switzerland, ya ambato wasu sauye-sauye da ka iya shafar rayuwa al'umma a fanin rasa wani bangare na aiyyukan yi.

Duk da irin ci-gaban da aka samu a duniya a fanin tattalin arziki masana na ganin ci-gaban na kara sauya yadda lamura ke tafiya inda kananan ayyuka ke kara bacewa. Misali ana kara neman hanyar tafiyar da shaguna ba tare da musu karbar kudi ba, da motoci masu tuka kansu, mai zai faru da milyoyin mutane idan ayyukan sun bace. Wannan na zama kalubale a kasashe masu karfin tattalin arziki.

DW.COM