Taron Shugabannin Turai kan rashin aiki | Labarai | DW | 27.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Shugabannin Turai kan rashin aiki

Shugabannin kasashen Turai sun yi alkarin tunkarar rashin aiki da matasa ke fuskanta.

Shugabannin kasashe na Kungiyar Tarayyar Turai sun yi alkawarin tunkarar rashin aiki da ke addabar matasan kasashen.

Sun bayyana haka yayin taro a birnin Brussels na kasar Belgium a wannan Alhamis, inda suke fuskantar matsin lamba na magance matsalolin rashin aikin matasa. Wasu alkaluma sun nuna yadda fiye da mutane milyan biyar da rabi mafi yawa 'yan kasa da shekaru 25 ke zaman kashe wando. Kasashen kamar Girka da Spain rashin aikin matasa ya kai makura.

Kafin tafiya wajen taron Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta shaida wa majalisar dokokin kasar cewa, ya zama tilas a tashi tsaye domin magance matslar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman