Taron Shugabannin Afirka a kan Cututtuka | Siyasa | DW | 15.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Shugabannin Afirka a kan Cututtuka

Kungiyar Tarayyar Afirka na nazarin sabbin hanyar tunkarar cutar Aids ko Sida da Zazzabin cizon Sauro da Tarin fuka, wadanda ke zama matsaloli mafi tasiri a cikin nahiyar.

Kama daga kasar Afirka ta Kudu da ke zaman kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar ta Afirka, ya zuwa ga 'yar uwarta ta Tarayyar Najeriya da ke da al'umma mafi yawa dama ragowar kananan kasashen da suka zauna suka kalli asarar miliyoyin al'ummominsu sakamakon jerin cututtuka irin na su HIV dai lokaci ya zo na neman sauyi.

Sauyi daga tsarin da ya maida nahiyar kan gaba ga batun cutar da yawan masu ita ya kai miliyan 23 cikin daukacin mutane 34 da ke duniya a baki daya masu dauke da chutar. Sauyi kan tsarin da maida kasashen mai dogaro ga agaji da magani daga Turawan Yamma a wajen yaki da daukacin annobar cikin tsawon kusan shekaru 10 da suka gabata.

Abin da kuma a cewar shugaban Najeriya kuma babban mai masaukin baki Goodluck Ebele Jonathan ya sanya sauyin zama wajibi domin kauce wa bala'in da ke iya fuskantar nahiyar a gaba.

"Lokaci ya yi na namijin yunkuri na hadin gwiwa domin fuskantar wadannan cututtuka. Tasirin su ta fannin rayuwar al'umma, da kisan kudi ga kauda ido ko kin daukar mataki dai zai zamo mai girman gaske gare mu. In har muna son samar da magani ga kowa, in har muna son cimma muradin karni to dole ne muyi wani abu daban. Ina matukar goyon bayan nahiyar Afirka ta sake kallon aikin gidanta da nufin neman mafita."

Mafitar kuma da daga dukkan alamu ke zaman jan aiki a tsakanin shugabanin nahiyar da yanzu haka ke dogaro da Turawan Yamma wajen samar da kusan kaso 90 cikin dari na bukatu na kudi da magungunan yakar cutukan a cewar Babatunde Osuntemehin da ke zaman wakilan Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a cikin zauren taron.

"Sama da kaso 90 cikin dari na mutanen da ke karbar magani suna samunsa ne daga kudaden kasashen wajen nahiyar. Ina jin muna bukatar raba nauyin. Ina jin muna bukatar kashe kudaden mu wajen maganin mutanen mu na Afirka."

Ana dai ta'alaka gazawar gwamnatocin da karuwar ta'azzarar cutukan da suke zaman babbar barazana ga kokarin nahiyar na cimma yan uwanta nahiyoyi ga batun ci-gaban tattalin arziki da zamantakewa.

To sai dai kuma a cewar Dr Mohammed Ali Pate da ke zaman karamin ministan lafiyar Tarrayar Najeriya dambu ne ke neman yin yawa ga harkokin gwamnatin.

To sai dai kuma koma ta ina mafitar ke akwai ga kokarin yakin dai wani abin da ya dauki hankalin taron na zaman na kasancewar Shugaban kasar Sudan Umar Hassan al-Bashir da ya bayyana a Abuja amma kuma yaki cewa kowa uffan.

Kungiyoyin fararen hula dai sun nemi Tarrayar Najeriyar da ta cafke shugaban domin mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka da ke zarginsa da laifukan yaki amma kuma mahukuntan Najeriyar suka ce ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa.

Farfesa Viola Onwuliri dai na zaman karamar ministar harkokin wajen da ke kula da kasashen Afirka a Tarrayar Najeriyar kuma a fadar ta Hassan al-Bashir din na Abuja ne a matsayin bako ga hukumar gamayyara kasashen Afirka ta AU.

"Ya zo taron Tarrayar Afirka ne, kuma Najeriya na Afirka, saboda haka Najeriya ba za ta saba bukatun AU ba".

Duk da cewar dai ya bayyana a zauren taron an bayyana shi a matsayin mutumin da bayanan a lokacin da aka nemi kasar ta Sudan ta yi wa taron na Abuja jawabi.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin