1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shekara shekara na jammiyar Labour a Birtania

Zainab A MohammadSeptember 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5M

Prime minista Tony Blair na Britanias yaki nuna alamun goyon bayansa wa ministan kula da harkokin kudi Gordon Brown, a matsayin mai gadan kujerarsa,duk da nanata tambayar sa da akeyi kann wannan batu.A hiran da yayi da gidan talabijin na BBC,Mr Blair dake halartan taron jammiyarsa ta Labour na shekara shekara na karshe,a matsayin shugaba,an nemi yayi bayani dangane da rahotan wata jarida data nunar dacewa bazai bada amanarsa wa Gordon Brown ba,a wajen taron na yini biyar.Mr Blair wanda a baya ya sha bayyana cewa Brown,zai kasance Prime minista wanda yasan makaman aiki,yace bazai shiga harkokin shugabanci ,kuma bashi da alaka da ita.Yace duk da irin rawa da Gordon Brown ya taka cikin harkokin cigaban Britania,dole ne kuma a bangare guda yayi laakari da rayuwar alumomin wannan kasa.Blair,wanda ya jagoranci jammiyar ta Labour tun daga 1994 dai,ya kasance shugabanta daya gudanar da zabubbuka guda uku a jere,cikin nasara.