Taron sassanta ′yan kasar Libiya. | Labarai | DW | 08.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron sassanta 'yan kasar Libiya.

Majalissar Dinkin Duniya na taro a Maroko domin sasanta bangarorin dake gaba da juna a kasar Libiya da nufin kawo karshen yaki a kasar.

A yau a kasar Maroko Majalissar Dinkin Duniya ke bude wani sabon zaman taro na neman sasanta bangarorin da ke hamayya da juna a kasar Libiya da zummar kawo karshen fadace-fadacen da ke yin barazana ga makomar kasar.Yanzu haka dai kasar ta Libiya na da gwamnatoci da kuma majalissu biyu ne ko wane daga nashi bangare.

Fraministan kasar Abdallah Al Tinni wanda kasashen duniya suka amince da sai da ta kaishi ga tserewa daga babban Birnin kasar Tripoli bayan da fadawarsa a hannun yan tawaye .Shugabannin kasashen Turai na ganin tattaunawa a karkashin inwar Majalissar Dinkin Duniya ce kadai hanyar da ka iya bada damar kafa gwamnatin hadin kan 'yan kasar ta Libiya.

A baya dai an sha irin wannan zama ba tare da cimma wata matsaya ba.To amma Majalissar Dinkin Duniyar ta ce a wannan karo ta na da kwarin guywar cewa kwalliya za ta biya kudin sabuni