Taron sasanta bangarorin Sudan ta Kudu ya ci tura | Labarai | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron sasanta bangarorin Sudan ta Kudu ya ci tura

Shugaba Salva Kiir ne ya ki ya saka hannu a kan yarjejeniyar wacce jam'iyyar da ke milki ta SPLM dama madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar suka saka amince da ita

Taron sasanta bangarorin kasar Sudan ta Kudu masu gaba da juna da ya gudana a jiya Litanin a birnin Adis Ababa ya watse baram baram wannan . Shugaba Salva Kiir wanda ke halarci zaman tattaunawar ne ya ki ya saka hannun akan takardar yarjejeniyar zaman lafiyar wacce wakilin jam'iyyar SPLM da ke milki a Sudan ta Kudun da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar kana madugun 'yan tawayen kasar wato Riek Machar suka saka wa hannu.

Hukumomin Sudan ta Kudin sun ki su saka hannu a kan yarjejeniyar ne domin shakkun da suka ce suna da a kan wani sashe na abunda ta kunsa. Sun ce suna bukatar su sake yin nazarinta kafin su bada na'am dinsu a kai. Shugaba Salva Kiir dai ya ce nan da kwanaki 15 masu zuwa zai sake dawo wa domin bayyana matsayin gwamnatinsa a kan wannan yarjejeniya.

A Litanin din jiya dai ne wa'adin da manyan kasashen duniya suka bai wa bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta Kudun na su sasanta ko su fuskanci takunkumai daban daban ya ke kawo karshe.