1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Ukraine sun gaza cimma matsaya

March 10, 2022

An gaza cimma matsaya a taron ministocin harkokin wajen kasashen Ukraine da Rasha, wanda ya gudana a birnin Antalya na kasar Turkiyya.

https://p.dw.com/p/48JZz
Turkiya | Kuleba, Lavrov, Cavusoglu - Taron ministocin kasashen waje a Antalya
TAttaunawar ministocin harkokin wajen Rasha da Ukraine a TurkiyyaHoto: Cem Ozdel/AA/picture alliance

Taron tsakanin mininstan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov dai, na zama na farko da manyan jami'an kasashen suka yi tun bayan da Rasha ta fara yaki da Ukraine. A cewar Kuleba babu wata nasara da aka cimma, ko yarjejeniyar tsagaita wuta ce ko da ta kwana guda da takwaransa Lavrov. Rashin cimma matsayar na da alaka da yadda Ukraine ta ki amincewa da wasu sharuddan Rasha, wanda ta bayyana su a matsayin mika wuya ne ga Rashar.

Karin Bayani: Rudani bayan fara yakin Rasha da Ukraine

A cewar ministan harkokin wajen Ukraine da alama Rasha ba za ta daina mamaya ba har sai ta cimma bukatunta. Gwamnatin Kyiv ka zalika ta yi watsi da bukatar Rasha na ta janye dakarunta, tare da ayyana yankin Crimea a matsayin wani bangare na Rashan da kuma amincewa da yankunan 'yan aware biyu da ke Donbas a matsayin masu cin gashin kansu. Sai dai kuma Kuleba ya ce a shirye yake ya sake ganawa da Lavrov domin tattauna hanyoyin kamo bakin zaren da ya yi makuwa.

Ukraine I Donetsk
Rasha dai na ci gaba da kai hare-hare UkraineHoto: Leon Klein/AA/picture alliance

Tuni dakarun Rasha suka isa da motocinsu masu sulki zuwa yankin Arewa maso Gabashin birnin Kyiv, a wani yunkurin na yi wa babban birnin Ukraine din kawanya. Ana shi bangaren ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kasashen da ke bai wa Ukraine makamai barazana ce ga kansu, kuma a shirye Rasha take ta tattauna batun tabbatar da tsaro ga Ukraine tare da kasashen Turai da ma ita kanta Rashar.

Karin Bayani: Rasha da Ukraine na son tsagaita wuta

Ko a baya dai an yi makamancin wannan tattaunawar a kasar Belarus tsakanin bangarorin biyu ba tare da cimma wata matsaya ba, sai dai ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya ce tattaunawar ta yau ta bude wani sabon babi ne na warwarewar lamura. Wannan tattaunawar na zama guda daga cikin wadanda aka tsara domin warware rikicin ta hanyar diflomasiyya, inda Isra'ila ma ke neman sassantawa ta hanyar tattaunawar kai tsaye da shugaban kasar Rasha Vladmir Putin da kuma Emmanuel Macron na Faransa da shi ma ke yawan kiran fadar Kremlin.