1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Ministocin harkokin wajen ƙungiyar tarayyar Turai

Tanko Bala, AbdullahiMarch 10, 2008

Ministocin tarayyar Turai sun baiyana fatan jamíyu masu raáyin Turai za su yi nasara a zaɓen Majalisun dokokin Sabiya

https://p.dw.com/p/DMIO
Dimitrij Rupel Ministan harkokin wajen ƙasar Slovenia wadda riƙe da shugabancin ƙungiyar tarayyar Turai.Hoto: AP Photo

Ministocin harkokin wajen ƙungiyar tarayyar Turai dake gudanar da taron su a birnin Brussels, sun ce sun yi amanna alúmar Sabiya za su goyi bayan jamíyu masu raáyin tarayyar Turai a zaɓe mai zuwa na majalisun dokoki da zaá gudanar, bayan rushe gwamnatin haɗin gwiwar sakamakon ɓallewar Kosovo wadda ta aiyana yancin cin gashin kan ta.

Da dama dai daga cikin mambobin ƙasashe 27 na ƙungiyar tarayyar Turan sun amince da yancin cin gashin kan na yankin albaniyawa wanda ya ɓalle daga Sabiya a watan da ya gabata. Tuni ma dai ƙungiyar tarayyar Turan ta fara tura tawagar jamián yan sanda dana shariá domin taimakawa kafuwar sabuwar yantacciyar ƙasar abin da ya haifar da mummunan ɓacin rai a Belgrade.

A ranar Asabar ɗin data wuce ne Firaministan ƙasar Vojislav Kostunica ya sanar da aniyar rushe gwamnatin haɗin gwiwar bayan da ya gaza tilasta ɗaukar shawarar yanke hulɗa da ƙungiyar tarayyar Turai matuƙar wakilan ƙasashen ƙugiyar suka suka goyi bayan yancin cin gashin kan Kosovo. A yanzu dai an sanya ranar 11 ga watan Mayu domin gudanar da sabon zaɓe.

Ministan harkokin wajen ƙasar Slovenia Dimitrij Rupel wanda ƙasar sa ke riƙe da shugabancin karɓa-karɓa na ƙungiyar tarayyar Turan yace yana fatan jamíyu masu raáyin tarayyar Turai za su sami nasara a zaɓen mai zuwa. "Yace yayin da wannan zaɓe ke gabatowa muna fata jamíyu masu raáyin Turai za su yi nasara, ina gani akwai alamu masu ƙarfafa gwiwa, mun ga ƙuriár jin raáyin jamaá mun kuma ga irin yadda ɗalibai suka yi ta zanga zanga. A saboda haka ban ga wata hanya mafi dacewa ba ga abokan mu na Sabiya face kasancewar su a cikin ƙungiyar tarayyar Turai.

Tun dai bayan ɓallewar Kosovo ake ta kai ruwa rana tare da zanga zanga da kuma hare-hare akan ofisoshin jakadanci na ƙasashe waɗanda suka goyi bayan aiyana yancin cin gashin kan. Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner yace Ministoci da dama na tarayaar Turai sun sha ƙoƙarin kai ziyara Belgrade to amma aka baiyana musu ƙarara cewa baá maraba da zuwan su.

Ministan harkokin wajen Sweden Carl Bildt shine Minista na farko na tarayyar Turai da ya kai ziyara Kosovo a ranar Asabar ɗin data gabata. Ya kuma shaidawa takwarorin sa a birnin Brussels cewa akwai rarrabuwar kawuna a tsakanin Albaniyawa masu rinjaye waɗanda ke kudanci da kuma Sabiyawa yan tsiraru a yankin arewacin ƙasar.

Wani muhimmin amari dake gaban Ministocin tarayyar Turan shine batun yankin gabas ta tsakiya. Babban jamiín harkokin wajen tarayyar Turan Javier Solana yace yana fatan cigaba da ƙoƙarin ciyar da shirin zaman lafiyar gabas ta tsakiya gaba, yace ya san ba abu ne mai sauki ba, to amma zasu cigaba, yace yana fatan tarzomar Gaza zata kawo ƙarshe.