Taron MDD kan tawayen Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 22.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron MDD kan tawayen Afirka ta Tsakiya

Kasashe 15 da ke da kujera a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na nazarin halin tawaye da ake ciki a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya domin daukan matakin da ya dace.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fara wani zama a birnin New-York da nufin nazarin halin da ake ciki a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya inda 'yan tawaye ke ci gaba da nausawa zuwa Bangui babban birni. Rahotannin da ke zuwa daga wannan kasa sun nunar da cewa gamayyar kungiyoyin tawayen Seleka ta karbe garin Bossangoua da ke gabashin kasar, da Kuma Damara da ke karkashin kulawar dakarun shiga tsakani na kasashen Afirka. Kakakin 'yan tawaye Eric Massi ya yi kira ga al'uma da su kwantar da hankulansu kafin isowar Seleka Bangui domin hambarar da shugaban wannan kasa wato Francois Bozize.

Wannan dai shi ne sumame na farko da 'yan tawayen suka kaddamar tun bayan fatali da yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma da gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya. Da ma dai sun dibar wa shugaba Bozize wa'adin laraba da ta gabata domin ya biya musu bukatunsu ko kuma su mayar da hannu agogo baya. Duk da cewa ya rattaba hannu akan dokar soke furzunonin siyasa da ke tsare, amma kuma 'yan tawayen sun nemi shi da ya sanya mambobinsu a cikin rundunar sojojin kasar kamar yadda yarjejeniyar su ta tanada.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar