Taron limaman Katolika a Jamus. | Labarai | DW | 20.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron limaman Katolika a Jamus.

Cocin Katolika ta Jamus ta fara gudanar da taro domin tantance kudin diyya ga yaran da limamanta suka ci zarafinsu

default

Limaman Katolika

Bisa matsin lambar da suka fuskanta, shugabannin cocin Katolika guda 27 a nan Jamus sun fara taron yini hudu a birnin Fulda na yankin tsakiyar kasar nan, domin tattaunna biyan diyya ga yaran da limaman cocin suka yi lalata da su a wani lokaci can baya. Limaman sun ce ba su tatance kudaden da za su bayar a matsayin diyyar ba. Wadanda wannan tabargazar ta shafa a mujami'ar garin Jesuit dai sun bukaci a ba kowannensu diyyar euro dubu 82, amma sai limaman suka ce sun daidaita kan ba da kashi daya daga cikin goma na wannan kudi. A farkon wannan shekarar ne dai aka fallasa tabargazar yin lalata da kananan yara da ta auku a cocin Katolika daga shekarun 1950 zuwa 1980.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Zainab Muhammad Abubakar