Taron Kungiyar Tsaro da Hadin kai a nahiyar turai a Berlin | Siyasa | DW | 28.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Kungiyar Tsaro da Hadin kai a nahiyar turai a Berlin

A yau ne aka bude taron yini biyu na kungiyar tsaro da hadin kai a nahiyar Turai OSCE domin bitar matsalar yaduwar kyamar Yahudawa a kasashen Turai

Tutar Kungiyar Tsaro Da Hadin Kai A Nahiyar Turai

Tutar Kungiyar Tsaro Da Hadin Kai A Nahiyar Turai

A lokacin da yake jawabin bude taron yau da sanyin safiya, shugaban kasar Jamus Johannes Rau ya bayyana takaicinsa a game da cewar an kira taron ne domin tattauna matsalolin da ake fama da su yanzun ba tare da ba da la’akari sauran matsaloli na tarihi ba. Ya ce sanin kowa ne cewar hatta bayan kawo karshen yakin duniya na biyu ba a cimma nasarar kawar da akidar nan ta wariyar jinsi da kyamar baki da kuma adawa da Yahudawa ba, walau a yammaci ko a gabacin Turai. Amma fa bai kamata wannan akida ta kabilanci da kiyayya ga baki da kuma kyamar Yahudawa ta gurbata yanayin zamantakewar jama’a a kasashen Turai ba. Gabatar da wasu dokokin da suka jibanci girmama hakin dan-Adam kawai ba zata wadatar ba, wajibi ne a yayata maganar, sannan su kuma wadanda alhakin al’amura ya rataya wuyansu su zama abin koyi ga sauran jama’a, a cewar shugaban kasar na Jamus Johannes Rau.

Kamar kuwa yadda aka saba a sauran tarurrukan kungiyar tsaro da hadin kai a nahiyar Turai OSCE, a wannan karon ma rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya, shi ne ya dabaibaye zauren tattaunawar. A cikin jawabinsa shugaban kasa Johannes Rau yayi gargadi a game da karuwar kyamar Yahudawa a sukan lamirin manufofin gwamnatin Isra’ila da ake yi. A nan wajibi ne a rika yin sara ana duban bakin gatari. Rau dai sai ya kara da cewar:

Ban dadara ba ina mai nanata yin kira ga dukkan masu sukan lamirin manufofin gwamnatin Isra’ila da rika ba da la’akari da mawuyacin hali na musamman da ake ciki. Tun bayan kafa kasar Isra’ila, al’umar kasar ke cikin hali na zaman dardar a game da makomarsu. Kuma ko da yake ba zata yiwu a dakatar da sukan lamirin wadannan manufofi ba, ko da da kakkausan harshe ne, amma fa wajibi ne korafin ya kasance akan basira da halin sanin ya kamata.

Kazalika dai a daya bangaren bai kamata a rika yi wa mutane tambarin kyamar Yahudawa ba saboda sukan lamirin manufofin gwamnatin Isra’ila. Tilas ne a samu banbancin ra’ayi tsakanin mutane ba tare da la’akari da kakkarfar dangantakar dake tsakaninsu ba.

A dai nasa bangaren, shugaban majalisar tsakiya ta Yahudawa Paul Spiegel yayi batu a game da kara yaduwar kyamar Yahudawa a nahiyar Turai kuma a saboda haka suke sa ran samun hadin kai daga taron na kungiyar OSCE. A lokacin da yake jawabi Spiegel karawa yayi da cewar:

Babu wani banbanci tsakanin masana dake amfani da manufofin Isra’ila don sukan lamirin Yahudawa da kuma irin furuce-furucen dake fitowa daga masu akidar wariya ko Musulmi masu zazzafan ra’ayi. Amma kuma a hakikanin gaskiya furuce-furucen na Musulmi masu zazzafan ra’ayi ba ya da ban tsoro kamar yadda lamarin yake dangane da yaduwar da ake samu ga kyamar Yahudawa a tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai.

Bisa ga ra’ayin Paul Spiegel, karbar sabbin kasashen da za a yi a kungiyar zai taimaka wajen samun cikakkun bayanai a game da azaba da kuma zautuwar da mutane suka sha fama da ita a karkashin mulkin ‚yan Nazi da ‚yan kwaminis.