Taron kungiyar kasashe renon Ingila a Uganda | Siyasa | DW | 22.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron kungiyar kasashe renon Ingila a Uganda

Sarauniyar Ingila tana Kanpala domin halartan taron kungiyar Commonwealth

default

Sarauniyar Ingila Elizabeth II

Gobe Juma’a ce in Allah ya kai ake sa rai cewar sarauniyar Ingila zata bude taron shugabanin kasashen kungiyar Commonwealth a birnin Kampala na kasar Uganda, kasar da Sarauniyar ta baro tun cikin 1954.

Wannan taro da za’a kammala shi ranar 25th ga wata, ana sa ran cewar shugabanin kasashe 53 na kungiyar ne zasu hallar ce shi, kuma zasu tautauna ne kan muhimman batutuwa da suka shafi cigaban rayuwar al’ummomin kasashe dake cikin kungiyar.

Duk da cewar akwai muhimman batutuwa da dama da mahalarta taron zasu tabo, batun daya fi daukan hankali shine batun kasar Pakistan, wacce kungiyar ta debarwa shugaban kasar Pervez Musharraf wa’adin kwanaki 10, kodai ya maido da kasar ga tafarkin dimukradiyya biye da sako yan adawa,ko kuma kungiyar ta dauki matakan hukunci na dakatar da itawanda zai kasance karo na biyu kenan Pakistan zata shiga tarihin kungiyar wacce aka dakatar har sau 2, bayan dakatarwa ta farko a 1999, zamanin da Musharraf ya kwace mulkin pakistan.

Kasashe kamar su Zimbabwe da suka shafe fiye da shekaru 4 basu tare da kungiyar, dakuma kasar Fiji da itama ta sami kanta a wajen kungiyar a shekarar bara sakamakon juyin mulki, suma dai ana kyautata zaton cewar za’a tabo su a yayin taron na gobe.

Shi dai wannan taro na kasashe rainon Ingila da akanyi dake gudana sau daya bayan shekaru biyu, wanda akayi na karshen sa a kasar Malta, inda a wancan lokaci akayi nazarin batutuwa da suka shafi cigaban rayuwar al’ummar kasashen da zummar ganin an kyautata rayuwar su.

Koda shike shugabanin a koda yaushe suka zauna cikin dandali sukan yi hankoron samun dauwamammiyar nasara ce cikin abubuwa dake gaban su kan shekara ta 2015, to amma har wannan lokaci akwai matsaloli masu tarin yawa daya kamata ace taron ya kawar dasu tun ba yau ba.

Bincike da kiddidiga ta nunar cewa matsalolin rayuwa, cututtuka, talaucci, rashin ruwan sha mai tsafta, karancin kiwon lafiya da makamantu, sunfi yin katutu ne a kasashe masu tasowa wanda yakamata ace tuni an rigaya an magance su.

Ga misali, kididigar da shirin majalisar dinkin duniya kan yakki da cutar kanjamau yayi kuma aka fito dashi wannan mako, ta nunar cewa a kowace rana ta Allah mutane dubu 5 ne da 700, kan mutu kodai ta hanyar ciwon kanjjamau, ko wata cuta makamanciyar ta,sa’anan wasu dubu 6 da 800, kan kamu da cutar a kowace rana.

Kazalika wata kididigar ta majalisar dinkin duniya ta nunar cewa a yankin gabacin Afirka ne akafi fuskantar mace macen mata masu juna, inda mata 880 kan rasa ransu wajen haihuwa tsakanin mata dubu 100 da kan haihu. To sai dai wannan kididigar ta kwatanta da kasar Sweden wacce mata biyu ne kadai kan rasa rayukan su daga cikin dubu 100, yayinda a kasar Canada mata shida kan rasu daga cikin dubu 100.

Don haka ne ake sa rai cewar shugabanin kasashen zasu dauki kwararan matakai dangane da hanyoyin kyautata rayuwar al’umma a waddan nan kasashe dake cikin kungiyar ta Commonwealth.