1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Kungiyar cinaki ta Dunia a Hong Kong

December 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvGk

Gobe ne idan Allah ya kai mu, a Hong Kong za a buda taron kungiyar Cinaki ta Dunia, wato WTO ko kuma OMC.

Saidai, a jajibirin wannan taro, a na kara samun rabuwar kanu, tsakanin kasashe dunia.

An ganawar sharen fage a yau, tsakanin tawagogin Amurika, Kungiyar Gammaya turai, Australia, Japon India da Brazil, da zumar kussanto ra´ayoyin kasashen, amma hakan ta faskra.

Baban batun da zai mamaye ajendar taron na gobe, shine na albarkatun noma.

Kasashe matalauta na dunia, na zargin kashashe masu arzikin masana´antu ,da karya masu lakadari, ta fannin cin gajiyar albarkatun noma.

Kasashen na Afrkia, Asia da kuma Latine Amurika, na zargin Amurika da turtai, da bada tallafi mai tsoka,ga manoman su, da kuma rufe kofofin su, abunda ke kara talauta, manoma a kasashe, masu tassowa.

Ko kamin a buda taron, da dama daga masharanta, a kan harakokin tattaln iarziki, da diplomatia, na hange cewar babu abinda zai tsinanawa.