Taron kolin shuagabannin KTT a Brussels | Siyasa | DW | 16.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron kolin shuagabannin KTT a Brussels

Babu wani ci gaba da aka samu dangane da kasafin kudin KTT a Brussels

Taron kolin KTT a Brussels

Taron kolin KTT a Brussels

Baki dai ya zo daya tsakanin shuagabannin kasashen kungiyar ta tarayyar Turai wajen Allah waddai da kalaman cin mutuncin kasar Isra’ila da suka fito daga bakin shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinajad da kuma karyata ta’asar kisan kiyashin da aka yi wa yahudawa da yake yi. A baya ga haka shuagabannin sun dace akan bai wa kasar Macedoniya wani matsayi na mai fafutukar da a karbe ta a wannan kungiya. To sai dai kuma duk da wannan ci gaba da aka samu a halin da muke ciki yanzun ba tabbas a game da ko shin shuagabannin zasu iya cimma wata daidaituwa akan kasafin kudin kungiyar ta tarayyar Turai dangane da shekara ta 2007 zuwa ta 2013 kamar yadda suka kudurta da farko. Bayan dai da suka kammala liyafar cin abincin rana shuagabannin sun shiga tattaunawa a wawware a bayan fage. A baya ga maganar kasafin kudin kungiyar, taron kolin kazalika ya mayar da hankalinsa akan rangwamen kudaden gudummawar da ake wa kasar Birtaniya da kuma shawarwari da Birtaniyar ta bayar a game da soke wani babi da kundin kasafin kudin na shekara ta 2007 zuwa ta 2013 ya tanadar. P/M Birtaniya Tony Blair na fatan ganin an dakatar da makudan kudin da kasashen kungiyar ke kashewa don karya farashin amfanin noma. Amma kasar Faransa daya daga cikin kasashen da suka fi cin gajiyar manufar ta karya farashin amfanin noma ta kiya kememe, inda ta ce ba zata yarda a aiwatar da wani canji nan da shekara ta 2013 ba. A daya bangaren kuwa ita Birtaniya sai kara fuskantar matsin lamba take yi domin ta ba da kai bori ya hau dangane da rangwamen gudummawar da ake mata. Tuni dai P/M Tony Blair ya bayyana shirinsa na yin gyara ga shawarar da Birtaniya ta bayar bayan tattaunawa ta bayan fagen da aka yi a wawware. Ana samun ci gaba sannu a hankali kamar yadda majiyoyi masu nasaba da wakilan Jamus dake halartar taron suka nunar. An saurara daga bakin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana mai fadin cewar:

A hakika ana fama da tafiyar hawainiya a tattaunawar da ake yi kuma da wuya a cimma tudun dafawa sakamakon banbance-banbancen ra’ayin dake akwai tsakanin kasashen a wawware. A dai halin da ake ciki yanzun ba za a iya hasashen yadda lamarin zai kaya ba.

Dukkan mahalarta taron dai ba da wata-wata ba suka amince da kasar Macedoniya domin kasancewa cikin jerin kasashen dake neman shigowa karkashin tutar KTT. Kazalika dukkan shuagabannin sun yi Allah waddai da lafuzzan cin mutuncin Isra’ila dake fitowa daga bakin shugaba Mahmud Ahmadinajad na kasar Iran, wanda ya musunta ta’asar kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa a nahiyar Turai yake kuma ba da shawarar maido da kasar Isra’ila zuwa nahiyar.