Taron kolin kungiyar AU ya dauki hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Taron kolin kungiyar AU ya dauki hankalin jaridun Jamus

Kokarin kame shugaban Sudan Omar al-Bashir ya mamaye zauren taron daya gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali kan taron kolin kungiyar tarayyar Afirka da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, musamman kokarin hana shugaban Sudan Omar al-Bashir ficewa daga kasar, yunkurin kuma da ya ci-tura.

A sharhin da ta yi jaridar neue Zürcher Zeitung ta fara ne da cewa shugaban Sudan Omar al-Bashir wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo, ya sake jefa hukumomin shari'ar na birnin The Hague cikin rudu. Ya kai ziyara Afirka ta Kudu amma gwamnati kasar ta kasa daukar wani mataki kansa. 'Yan adawar Sudan da ke kaura da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce wannan wani abin kunya ne. Sai dai a cewar jaridar ba Afirka ta Kudu kawai ce ta kasa yin wani katabus game da batun na al-Bashir ba, hatta Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kwashe tsawon shekaru bai yi wani abin a zo a gani ba. Amma ba nan gizo ke tsaka ba. Sudan dai na daya daga cikin kasashe kalilan na Afirka da ke da kwanciyar hankali, ta kuma ba da mafaka ga dubun dubatan 'yan gudun hijira sannan tana cikin yakin da ake yi da 'yan ta'addanci. Watakila saboda haka ne wasu majiyoyin diplomasiyya ke cewa in ba don shugaba al-Bashir ba da Sudan ta ruguje kamar Libya, watakila wasu 'yan siyasar yammacin duniya suna murna ganin ba a mika al-Bashir ga kotun ta birnin The Hague.

Mugabe gwarzon Afirka na gaske

Mugabe gwarzonmu inji jaridar Die Tageszeitung tana mai cewa a matsayinsa na jagoran taron kolin kungiyar AU a Afirka ta Kudu, shugaban Zimbabwe ya yi amfani da kalaman da suka dace inda ya ce dole ne Afirka ta ceto kanta da kanta. Wannan furucin ya sha yabo daga bangarori da dama.

AU Gipfel in Adis Abeba Äthiopien 2015

Robert Mugabe na Zimbabwe

Shugaba Robert Mugabe ya yi nuni da cewa yanzu lokaci ya yi da Afirka za ta hada kai kana ta daina zargin kasashe masu ci gaban masa'antu da laifin hannu a matsalolin da nahiyar ke fuskanta. Jaridar ta ce Mugabe da ke zama shugaban kungiyar AU a yanzu ya yi kira da a zuba jari mai yawa a fannonin sufuri jirgin kasa da na sama da fasahohin kwamfuta domin Afirka ta raya kanta da kanta. 'Yan Afirka da yawa na kallon Mugabe a matsayin gwarzon Afirka duk da sanin cewa da yawa daga cikin 'yan kasarsa sun yi kaura zuwa kasashen ketare don neman ingantuwar rayuwa.

Kokarin yi wa tsarin mulkin kasa kwaskwarima

Yanzu haka daukacin al'ummar kasar Ruwanda na mahawara game da makomar shugaban kasarsu, inji jaridar Die Tageszeitung.

Paul Kagame

Shugaba Paul Kagame na Ruwanda

Ta ce a cikin shekaru biyu masu zuwa za a gudanar da zabuka a Ruwanda, inda bisa kundin tsarin mulkin kasa shugaba Paul Kagame wanda ya ja ragamar mulki har wa'adi biyu ba zai iya sake tsayawa takara ba. Kagame wanda a 1994 ya jagoranci wani yakin sunkurun da ya kawo karshen kisan kiyashin da aka yi wa kabilar Tutsi, tun a shekarar 2000 yake shugaba, an zabe shi karon farko a 2003 sannan aka sake zabansa a 2010. Yanzu masu fafatukar na shirya wani kundi dauke da sa hannun mutane miliyan 3.7 daga miliyan 12 na al'ummar kasar don canja tsarin mulkin kasar don Kagame ya sake tsayawa takara. Wannan ba abin mamaki ba ne domin a makwabciyar kasar wato Burundi shugaba Pierre Nkurunziza na neman sabon wa'adin mulki na uku, matakin da ya jefa kasar cikin rudani. Sai dai sabanin Nkurunziza, Kagame na matsayin wani jarumi wanda ya ce a shirye yake ya mika kanshi ga bukatun al'ummarsa.