1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Makomar tsaron yankin kasashen Larabawa

Mahmud Yaya Azare AH
March 19, 2026

Shugabannin ƙasashen Larabawa da na Musulmi na gudanar da wani muhimmin taro a birnin Riyadh na Saudiyya domin tattauna makomar tsaron yankin.

https://p.dw.com/p/5AhpT
Hoto: Qatar News Agency/REUTERS

Taron da ke zuwa adaidai lokacin da kasar ta Iran ke kai hare haren ramuwar gayya kan tashar iskar gas da ke birnin Riyadh da kuma wasu cibiyoyin gas din a kasashen Qatar da Bahrain, don ramuwar gayya ga harin da Isra'ila ta kai wa kasar ta Iran kan babbar tashar samar da man fetir dinta ,manufar sa shi ne kashe wutar.

Rikicin da tsawaitarsa kan iya durkusar da tattalin  arzikin kasashen yankin da ma jefa duniya cikin balahirar tsadar makamshi. Kuma kamar yadda ministan harkokin wajen Saudiyya,Faisal Bin Farhan ke cewa,kasar ta Iran ta wuce makadi da rawa wajen huce haushinta kan kasashen yankin na Gulf:

“Kasashen da muke halartar wannan taron muna kara nunawa Iran kuskurenta kan hare-haren ramuwar gayyar da take kawo mana,wanda kwamatin sulhu na MDD ya yi wa tofin Allah tsine.Muna kira da ta sake lissafi ta dakatar da kai hare- hare kan kasashenmu. Domin yin hakan yana kara tunzura kasashenmu,da kara mata bakin jini,da kara mai da kanta saniyar ware.”

Katar | Sondergipfel der Arabischen Liga nach israelischem Luftangriff | Syrischer Präsdient al-Sharaa
Hoto: Qatar News Agency/REUTERS

Shi ma ministan harkokin wajen  Turkiyya, Hakan Fidan,wanda ya nemi Iran din da ta takaita kai hare-haren ramuwarta kan Isra'ila da jiragen ruwan Amurka da ke kan Teku,don kaucewa batawa da makwabtanta da dagulewar lamura a yankin,ya nemi mahalarta taron da su matsa lamba don kawo karshen yakin nan take a yankin,yana mai gargadinsu da cewa:

“Manufar kaddamar da wannan yakin kan Iran bai takaita kan rusa gwamnatin Iran da durkusar da kasar ba,har ma da kokarin baza ikon Isra'ila a kasashenmu,don haka dole mu tashi mu farga.”

Saudi-Arabien Dschidda 2025 | Außerordentliche Sitzung der Organisation für Islamische Zusammenarbeit
Hoto: Amer Hilabi/AFP/Getty Images

To sai dai ministan harkokin wajen Oman ya ce,duk da cewa,abun takaici ne hare- haren da Iran ke kai wa makwabtan nata,ciki har da kasarsa, amma ya kamata a yi wa kasar ta Iran gargadin tsaida yakin.