1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Kasashen Turai da Afrika

Halima AbbasDecember 7, 2007

Taronkasafin kudin Afrika

https://p.dw.com/p/CYtN
Africa

Birnin Lisbon, ƙasar Portugal yayi haramar karɓan baƙoncin taron shugabnannin ƙasashen Turai da Afrika wanda shine farkon irinsa tun daga shekaru bakwai da su ka gabata.A jiya alhamis an buɗe taron shawarwarin kuɗi da zuba jari a Afrika da nufin samar da hanyoyin taimaka wa ma’aikatu masu zaman kansu yadda za su taka rawar da shugabanninsu ke son gani daga garesu kamar yadda ya ke shinfifiɗ a cikin shirinsu. Halima Balaraba Abbas na da ƙarin bayani.

“Muna batun bunƙasa aikin noma a yankin Darfur. Amma akwai babban haɗari a wannan yanki a hannu daya.A dayan hannun kuma ana zuba kudaɗe da dama a wannan yanki sabo da man fetur da kuma wasu abubuwa daban.To ta ƙaƙa za mu iya aiwatar da haka.

Clvin Miller kenan na hukumar abinci ta duniya .Ya yi misali da Sudan a matsayin ƙasa da masu zuba jari daga ƙasashen waje ke kauce mata ko da ya ke akawai kwanciyar hankali a saasan ƙasar da dama tare da da fagage masu albarka. Akawai wasu kamfanoni da ke daukan mataki akan taken wannan taro wanda shine, Buɗe sukunin zuba jari a Afrika.Kanfanin Info Tera na ƙasar Birtaniyaya ta haɗa rahotanni a game da tasawirar ƙasar ta taurarin ɗan adam da sauran fasahohi. kuma yana gudanar da ayyyuka da dama a ƙasar Angola.

Simon Ashby ya ce ba a anfani da filye da maadinai yadda ya kamata a Afrika sabo da rashin sahihan rahotanni.

“Ashby ya ce yan Afrika yan kalilan ne ke mallakar filaye. Bankin duniya da kungiyar Tarayyar Turai suna daukar matakan magance wannan matsala.Mun samar da shirin nomar rani wanda abu ne na azo a gani.To amma idan aka bukaci in taimaka wa wannan shiri da dola ɗari babu makawa zan nuna shakku.Ƙasashen irinsu Angola sun fara ne sannu sannu da gurin samun ci gaba..Mu na hangen cewa za a dauki shekara 25 zuwa 30 nan gaba wajen magance matsalar filaye.

Jose Amario Tati gwamnan jihar Bie ta ƙasar Angola inda kanfanin Info Tera ke aikin keɓe filayen aikin noma da gina gidaje ya ce yakin basasan da ya adadabi ƙasarsa ya dakatar da zuba jari a cikinta in ba a baya bayan nan ba.

“Ya ce an kwashi shekaru aro aro ana kallon yawancin kasashen Afrika a matsayin inda ake fama da nauoiin balai .Kuma bai kamata a koka a game da rashin zuba jari ba dubi ga rahotannin yaki da ake ji a game da Afrika.

Edith Miller babban darektan kungiyar EMRC da ke tafllafa wa wannan taro ta ce ana bukatan kawar da shingaye da dama muddin ana son bunkasa maaikatu masu zaman kansu a masayin makamin samar da ci gaba.

Ta ce kasashen Turai suna shakku a game yin hulɗar kasuwanci da Afrika. Dalilin kenan da ya sa ya zama tilas dan kasuwa ya nemi visar zuwa Turai. Akwai wasu yan kananan matsaloli da kasashen turai kansu basu da masaniya a game da su.Dalili kenan da ya sa hukumar zantaswa ta kuniyar Tarayyar Turai bata samun nasara.

Olophe Babatkingi Rabaki daga ƙasar Benin na daya daga cikin yan Afrika da za su halarci taron na birnin Lisbon. Yana da kwazon aiki kamar dai sauran takawarorinsa yan Afrika.Yana aiki ne a fannonin muɗabbaa da motoci.

“Ya ce za a samu anfani mai ɗinbin yawa ta yin haɗin gwiwa tare da ƙasashen Turai .Amma abin da ke da muhimmaci shine sake yin anfani da kudin da ke akwai wajen tallafa wa ayyukan a Afrika.”

Wakilan Turai da na Afrika a gun wannan taro sun yarda cewa ana bukatan samar da jari don maaikatu masu zam kansu su iya su taka rawar da gwamnatocinsu ke bukata. A gobe asabar ne idan Allah ya kaimu za su bayyanar da haka a cikin shelar da zasu tantance akanta a yau jumaa.