Taron kasashen dunia a game da dumamar yanayi a birnin Montreal na Kanada | Labarai | DW | 28.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashen dunia a game da dumamar yanayi a birnin Montreal na Kanada

A birnin Montreal na Kanada, yau ne kasashe 180 daga sassa daban daban na dunia ke fara zaman taro bisa gayyatar Majalisar Dinkin Dunia.

Babban makassudin wannan garagaramar haduwa, da za ta dauki tsawon sati 2,shine na nemo hanyoyi da matakai, domin yaki da dumamar yanayi, da ke matsayi barazana, ga rayuwar jama´a a duniar mu ta yau.

Kurrarun massana illimin mahhalli, za su bitar matsaloli da dunia ke fuskanta, ta wannan fanni, da kuma duba yiwuwar faddada yarjejeniyar yaki da gurbacewar mahhali da su ka rattaba hannu a kan ta, a birnin Kyoto.

Saidai wannan taro, na samun tarnaki daga kasar Amurika, wadda a shekara ta 2001, ta yi watsi da yarjejeniyar ta Kyoto , kuma a yalin yanzu ta jaddada matsayinta na kauracewa dukan mahaurori da su ka shafi yaki da gurbacewar yanayi.