Taron kasashen ASEAN | Labarai | DW | 15.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kasashen ASEAN

Shugabanin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya sun rattaba hannu akan yarjejeniyar habaka harkokin samarda makamashi tare da samar da hanyoyi daban na samun makamashin baya ga anfani da mai.

Wannan yarjejeniyar ita ta kawo karshen taron mako guda na kungiyar a kasar Phillipines,inda aka tattauna batutuwa da dama da suka shafi masifu,cututtuka da taaddanci.

Taron ya kuma duba batun inganta dangantaku tsaknin Sin da Japan.