Taron kasa a Najeriya -nasara ko bata lokaci? | Siyasa | DW | 21.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron kasa a Najeriya -nasara ko bata lokaci?

Bayan kammala taron kasa a birnin Abuja, tambayar da ake ita ce shin ya samu nasarar cimma muradunsa ko kuwa wani zagaye ne na bata lokaci da ma dukiyar Najeriyar?

Taron kasar na Najeriya dai ya kasance dankali sha kushe ga mafi yawan al'ummar kasar wadanda bayan nuna rashin halarci da ma cancantarsa ya kasance dandalin kokarin kaiwa ga iko da arzikin kasar da ma yadda za a juya akalarta a nan gaba bisa ga shawarwarin da aka cimmawa.

Taron da mahukunatan Najeriya suka dage kan cewa sun shiryashi ne domin nemo hanyoyin sulhunta dimbin matsalolin da suka dade suna adabar Najeriya musamman kokarin yi wa al'umma saiti don komawa a kan turbar Najeriya kasa daya al'umma daya. To sai dai yadda aka ringa nuna wa juna 'yar yatsa a tsakanin mahalarta taron da kuma da kyar aka kaucewa watsewa baram-baram ya sanya Dr. Jibo Ibrahim manazarci a kan harkokin da suka shafi Najeriya bayyana cewa ai tun ran gini ran zane.

"Na farko mutanen nan ba su fahimci dalilin zuwansu taron nan ba. Yadda aka zabi mutanen nan ba a nuna gaskiya ba domin kowa ya san mutanen arewacin Najeriya sun fi yawa, amma sai aka tura mutanen wani yanki suka fi yawa a taron. Nuna bambamcin da ake maimakon ya ragu sai ya karu. Abu na biyu shi ne sun jawo rikici da yawa a kan batun yadda za a raba kudin kasar nan, kuma wannan rikicin da suka tayar zai damu jama'ar kasar nan sosai."

Kammala taron lafiya ya zama abin mamaki

Nigeria Goodluck Ebele Jonathan Komitee zur Vorbereitung der Nationalen Konferenz

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da wakilan kwamitin shirya taron kasa

Ko da yake an kammala taron cikin kwanciyar hankali har ma an mika kamalallen rahoto, ya kasance bazata ga mutane da dama, musamman yadda yanayin bangaranci ya bayyana a fili da ma gaza samun nasara a yunkurin rubuta sabon tsarin mulki da wasu wakilai suka bullo da shi, abinda ya kara karfin masu zargin an shirya taron ne bisa wata manufa.

Wannan ya sanya wasu masharhanta kalon taron a matsayin wanda ya gaza cimma bukatun kafa shi. To sai dai ga Mallam Sulke Yahya Hamma dattijo daga arewacin Najeriya na mai ja a kan wannan domin ya ce akwai abinda aka koya kuma zai zama darasi domin gaba.

‘"Na farko ya zaburar da mu kan cewa zaman tarayyar Najeriya da kuma tsere na zamantakewa a tsakaninmu da abokan zamanmu yana nan da zafinsa kuma yana bukatar natsuwa. Na biyu an zo da tanadi a canza tsarin zamantakewar kasar da salon mulkinta da damar da 'yan siyasa da shugabannin gwamnati ke da ita a 2015 mai zuwa ta fannin zabe."

Aiki da rahoton babban taron na Najeriya

Alhaji Gambo Jimeta, Justice Mamman Nasir und Chief Edwin Clark

Lokacin zaman muhawara a taron kasa

A yayin da ra'ayoyi suka sha bambam a kan sakamakon taron kasar na Najeriya da ake korafin yawan makudan kudin da aka kashe a kansa, saboda tunanin tasirin rahoton taron ga makomar Najeriya, ga Dr. Jibo Ibrahim ya ce bai ga abin daga hankali a kai ba.

"Wannan ba damuwa tun da rahoton da suka yi an san abinda zai same shi don ai akwai wani daki a ofishin sakataren gwamnatin Najeriya inda in aka jefa shi aka kulle shi ke nan sai bayan wasu shekaru biyar a sake kiran wani taron. Yanzu ma ai ba lokacin da za a kai wa majalisar dokokin tun da lokaci ya kure."

Gaza samun nasarar shigar da batun karin wa'adi ga shugaban kasa da ma sabon tsarin mulki na zama abinda ake wa kallon babbar koma-baya ga wadanda suka fake da taron don cimma wannan buri.

Abin jira a gani shi ne mataki na gaba da mahukuntan Najeriyar za su dauka a kan sakamakon taron da a yanzu iko ya koma hannun majalisar dokokin kasar wacce al'ummar kasar za su zura wa idanu a yanayi na kifi na ganinka mai jar koma.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idriss
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin