1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kafofin yada labarun duniya da DW ke shiryawa

July 3, 2014

A taron na Global Media Forum da a bana ya kasance karo na bakwai, an tattauna daga matakin watsa labaru zuwa shiga a dama da ku - kalubale ga kafofin yada labaru.

https://p.dw.com/p/1CV4Q
GMF Global Media Forum 2014
Hoto: DW/J. Kabir

Mutane kimanin 2000 daga kasashe 100 da suka fito daga bangarorin rayuwa daban-daban kamar na kafofin yada labaru da 'yan siyasa da 'yan kasuwa da kuma masu ilimin jami'a, sun kwashe tsawon kwanaki uku suna tattaunawa tare da tabka muhawarori game da kalubalen da duniya ke fuskanta na ci gaba, da muhimmiyar rawar da jarida ke takawa a ciki.