Taron Jeniva a kan batun nukiliya na Iran | Labarai | DW | 08.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Jeniva a kan batun nukiliya na Iran

Ministocin harkokin waje na ƙasashen Faransa da Jamus da Ingila sun isa Jeniva domin tattauna batun shirin nukliya na Iran tare da takwaransu na Amirka John Kerry.

Sakataran na harkokin wajen Amirka John Kerry ya katse ziyarar da yake a yankin Gabas ta Tsakiya domin halartar taron wanda babbar kantomar Ƙungiyar Tarrayar Turai kan manufofin ƙetare Catherine Asthon da kuma MDD ke jagoranta.

Ana sa ran a wannan ganawa ta manya ƙasashen duniyar guda biyar haɗe da Jamus,za a cimma wata yarjejeniya ta tarihi bayan da aka kwashe shekarun da dama shirin na gamuwa da cikas. A wani tayin sassantawa kan batun da ba bayyana ba yazuwa yanzu, Iran ta amince ta yi watsi da wani ɓangare na shirinta na nukiliya da kishi 20 cikin ɗari. To amma firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce babban kuskure ne mai tarihi kasashen duniyar zasu yi, idan suka amince da tayin na Iran.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu